Dalilin da yasa 'yan ta'adda ke ta kai wa Kaduna farmaki, Tsohon daraktan DSS Ejiofor

Dalilin da yasa 'yan ta'adda ke ta kai wa Kaduna farmaki, Tsohon daraktan DSS Ejiofor

  • Tsohon daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, Mike Ejiofor, ya ce akwai bukatar sauya tsarin tsaro a kasar nan
  • A cewarsa, dalilin da yasa 'yan ta'adda ke yawan kai farmaki Kaduna ba ya wuce alaka da son bata sunan gwamnati ganin zabe ya gabato
  • Ejiofor ya ce suna kai farmaki Kaduna har manyan wuraren tsaro na kasar nan domin su nuna cewa babu inda ba za su iya shiga ba tunda suka shiga wuraren nan

Jerin hare-haren da 'yan ta'adda suka dinga kai wa jihohin Kaduna da na Niger a cikin kwanakin nan yasa 'yan Najeriya sun fara tantama kan tsarin tsaron kasar nan.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, baya ga haka, lamarin yasa jama'a na tambayoyi kan yadda 'yan ta'addan ke cin karensu babu babbaka inda suka alakanta hakan da sakacin gwamnati wurin kawo karshen lamarin.

Kara karanta wannan

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

Dalilin da yasa 'yan ta'adda ke ta kai wa Kaduna farmaki, Tsohon daraktan DSS Ejiofor
Dalilin da yasa 'yan ta'adda ke ta kai wa Kaduna farmaki, Tsohon daraktan DSS Ejiofor. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Tsohon daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, Mike Ejiofor, ya yi magana kan abinda zai iya zama dalilin da yasa 'yan ta'addan ke cin karensu babu babbaka a arewacin Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, "Ina tsammanin ya dace mu sauya tsarin tsaronmu. Mun bar mutanen nan suna cin karensu babu babbaka da rana tsaka. Idan da an tura jirage marasa matuka, ya dace a gano inda miyagun suke.
"A kowacce rana muna jin cewa an halaka mutum 50, 1,000 amma ba mu ganin gawawwakinsu kuma ba a kama ko daya daga cikinsu. Ya dace a bayyana gawawwakinsu da kuma wadanda aka kama."

Kamar yadda Ejiofor yace, dalilin da yasa 'yan ta'addan ke yawan kai farmaki jihar Kaduna shi ne ganin irin tsaron da ka jihar da hukumomin da ke jihar. Hakan tamkar jan kunne ne na cewa suna iya kai farmaki a jiha irin Kaduna balle sauran jihohin arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

"Dalili na farko dai ba ta sunan gwamnati suke son yi tare da rage wa jama'a kwarin guiwa kan gwamnati balle da zabe ke karatowa.
"Kada ku manta, wadannan jama'ar basu taba sanar da 'yan Najeriya abinda suke bukata ba. Kawai tada hankula suke yi. Na kuma yarda cewa dalilinsu na yawan kai hari Kaduna shi ne ganin yadda barikokin sojoji suke.
"Kada ku manta, sun shiga filin sauka da tashin jiragen sama. Sun kai farmaki makarantar horar da hafsoshin soji. Sun kai wa titin dogo, wasu manyan makarantu tare da sace mutane. Idan har za su iya addabar Kaduna, babu inda ba za su iya shiga ba. Aika sako kawai suke ga gwamnati."

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

A wani labari na daban, mai martaba Sarkin Onitsha na Jihar Anambra, Mai Martaba Igwe Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe, ya bayyana yadda ya kubuta daga hawan jirgin Abuja zuwa Kaduna da ‘yan ta’adda suka kai wa farmaki a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sarkin zai hau jirgin amma kiran wayar da aka yi masa na wasu mintina yasa ya rasa hawan jirgin.

A wannan rana mai muni ne ‘yan ta’adda suka kai farmaki kan jirgin kasan da ya taho Kaduna. Sun jefa bama-bamai a kan layin dogo, lamarin da ya tilasta wa jirgin tsayawa, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng