Najeriya bata taba samun shugaban kasa irin Buhari ba tun daga 1914, in ji wani gwamnan arewa
- Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya jinjinawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Masari ya ce Najeriya bata taba samun shugaban kasa kamar Buhari ba tun da aka kafata a 1914
- Martanin gwamnan na zuwa ne a yayin da ake tsaka da fama da rashin tsaro a kasar
Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mafi nagarta da Najeriya ta taba samu.
Masari ya bayyana cewa tun bayan hade Najeriya a 1914, kasar bata taba samun gwamnati mai inganci da shugaban kasa kamar Buhari ba, Premium Times ta rahoto.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 2 ga watan Afrilu, a Katsina yayin wani gangami da wadanda suka amfana da shirin tallafi na gwamnatin tarayya wato NSIP a jihar suka shirya, rahoton PM News.
Gwamnan na Katsina ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya shimfida ginshiki mai nagarta, kuma idan har gwamnatin gaba ta yi amfani da shi yadda ya kamata, yan Najeriya da dama za su fita daga kangin talauci.
A cewarsa, shirin NSIP ya rage wahalhalun da yan Najeriya da dama ke fuskanta kamar na tunanin abun da za su ci.
Ya kara da cewar shugaban kasar ya cancanci yabo da samun goyon baya kan shirin da babu gwamnatin da ta taba tunanin samar da shi.
Masari, wanda ya goyi bayan Buhari ya mayar da shi doka kafin karshen mulkinsa, ya ce idan aka yi hakan, shirin zai zama na din-din-din kuma babu gwamnatin da za ta zo ta tsayar da shi.
Takarar shugabancin Tinubu ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar arewa
A wani labarin, mata da matasa da dama a fadin jihohin arewa 19, a ranar Juma’a, sun yi tururuwa a Abuja domin marawa jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu baya.
Sun nemi a tsayar da Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar mai mulki a zaben shugaban kasa mai zuwa, Daily Trust ta rahoto.
Har ila yau, sun bayyana cewa Tinubu ne mutum daya tilo da ya cancanta kuma zai iya a cikin dukkanin masu takarar da suka ayyana kudirinsu na son daidaita tattalin arzikin kasar.
Asali: Legit.ng