2023: Yahaya Bello Ya Yi Alƙawarin Mayar Da Ƴan Najeriya Miliyan 20 Attajirai Idan Aka Zaɓe Shi Shugaban Ƙasa
- Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi a ranar Asabar ya fito fili ya bayyana ra’ayinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023
- Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a Eagle Square da ke Abuja inda ya ce zai mayar da ‘yan Najeriya miliyan 20 miloniyoyi
- A cewarsa, a lokacin da jam’iyyar PDP take mulki, rahotanni sun nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 100 ne ke rayuwa cikin matsananciyar fatara amma yanzu a mulkin APC yawan ya koma miliyan 70
FCT, Abuja - A ranar Asabar, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ta bayyana wa kowa shirinsa na son tsayawa takarar shugaban kasa a 2023, The Cables ta rahoto.
Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a Eagles Square da ke Abuja inda ya ce zai dada daga inda shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya, ta hanyar mayar da ‘yan Najeriya miliyan 20 miloniyoyi zuwa shekarar 2030.
Ya ce zai ci gaba ne daga inda Buhari ya tsaya
Kamar Vanguard ta nuna, Gwamnan ya shaida cewa:
“Bisa rahoton BBC na ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 2012, fiye da ‘yan Najeriya miliyan 100 suna rayuwa ne cikin fatara lokacin jam’iyyar PDP ce take mulki.
“Yayin da APC ta amshi mulki, rahoton ya nuna cewa yawan mutanen ya koma miliyan 87 a shekarar 2018 duk da dai Najeriya ta zarce Indiya inda ta zama kasa mafi talauci a duniya.
“Cikin wata daya kacal, Najeriya ta sauya inda ta mayar wa Indiya matsayintsa bisa kokarin shugaban kasa inda yawan mutanen ya koma 70m. Hakan yana nuna cewa a hankali gwamnati tana tsamo mutane daga talauci.”
Kamar yadda ya shaida, gwamnatin Buhari tana da shirin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga cikin fatara zuwa shekarar 2030.
Manyan mutane da dama sun halarci taron
Hakan yasa Yahaya Bello ya ce yana da shirin mayar da ‘yan Najeriya miliyan 20 miloniyoyi zuwa shekarar 2030 sannan ko wannensu zai bai wa mutane 5 tallafi.
Taron da ya shirya ya samu halartar mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, mataimakin gwamnan Jihar Kogi, Edward Onoja da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da sauransu.
Diyar wanda ake zargin ya lashe zaben shugaban kasa na 1993, marigayi Moshood Abiola, Hafsat Abiola-Costello, ce aka nada wa mukamin darekta janar ta kamfen din Yahaya Bello na neman shugaban kasa.
Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023
A wani labarin, Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya shiga jerin ‘yan takaran shugaban kasa a zaben 2023 da ke karatowa bayan an kwashe watanni ana tsegunguma, Vanguard ta ruwaito.
Har yanzu dai bai fito a mutum ya bayyana cewa yana neman kujerar karara ba, amma an saki wani littafi a cikin kwanakin karshen makon nan wanda ya kambama shi.
An zabi jagoran jam’iyyar APC din, Amaechi har sau biyu, inda ya rike kujerar gwamnan Jihar Ribas a karkashin jam’iyyar PDP, amma kuma ya bar jam’iyyar kafin zaben 2015.
Asali: Legit.ng