An Gurfanar Da Wani Mutum a Kotu Kan Satar Biskit Na N1,250 Daga Kanti
- Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta gurfanar da wani mutum mai shekaru 31, Sunday Hungbeji ranar Laraba a gaban kotu akan sata
- Ana zarginsa da satar biskit mai kimar N1,250 a wani shago yayin da ya boye shi a aljihunsa ba tare da sanin cewa kamarar CCTV ta dauke shi ba
- Yayin da ya zo fita, jami’an tsaron shagon sun tunkare shi inda ya gaza bayani akan yadda biskit din ya shiga aljihunsa daga nan suka mika shi ga ‘yan sanda
Jihar Legas - A ranar Laraba an gurfanar da wani Sunday Hungbeji mai shekaru 31 gaban wata kotun majistare ta Badagry bisa zarginsa da satar wani biskit (Shortbread) mai kimar N1,250.
Duk da dai ba a bayyana adireshinsa ba, amma yanzu haka yana fuskantar tuhuma a gaban kotu akan sata, Premium Times ta ruwaito.
Wanda ake zargin bai amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa ba.
Mai gabatar da kara, Akpan Nko, ya sanar da kotu cewa wanda ake zarginsa ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022 da misalin karfe 6:00 na yamma a Beach Town Mall, mai lamba 1, Joseph Dou Way, Badagry, Jihar Legas.
Nko ya ce wanda ake zargin ya saci biskit (shortbread) din mai kimar N1,250 a Beach Town Mall.
Kotun ta bayar da belinsa
Kamar yadda Premium Times ta nuna, Nko ya shaida wa kotu cewa:
“Wanda ake zargi ya shiga shagon sannan ya sace biskit din, sai ya boye shi a aljihunsa ba tare da sanin cewa kamarar CCTV ta dauke shi ba.
“Yayin da ya fita, sai jami’an tsaron shagon suka fuskancesa kuma suka kama shi da biskit din a cikin aljihunsa.
“Yayin da ya kasa kare kansa akan yadda biskit din ya shiga aljihunsa, take anan suka kama shi sannan suka mika shi ga ‘yan sanda don a yanke masa hukunci.”
Ya ci gaba da cewa laifin ya ci karo da sashi na 287 na dokar masu laifin Jihar Legas na shekarar 2015.
Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya ya bayar da belin wanda ake zargin a N50,000 sannan ya bukaci ya gabatar da tsayayye kuma mai aikin yi.
Har ila yau, ya dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Afirilu.
Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Asali: Legit.ng