Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba
- Gwamnatin jihar Kaduna ta sake yin bayani game da harin da 'yan ta'adda suka kai kan jirgin kasan Abuja-Kaduna
- An kai hari kan wani jirgin kasan fasinjoji a hanyar Abuja, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dama
- Ya zuwa yanzu, an ce ba a san adadin mutanen da harin ya rutsa da su ba bisa bayanan da aka samo daga hukumar NRC
Kaduna - Fasinjoji da yawa da suka shiga jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka kai wa hari a daren ranar Litinin, har yanzu ba a tantance yawansu ba, a cewar gwamnatin jihar Kaduna.
Idan baku manta ba, wasu mabarnata sun yi aika-aika kan fasinjoji da dama a cikin wani jirgin da ya taso daga babban birnin tarayya zuwa jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin kasar nan a daren Litinin da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin tsayawa.
Bayan haka ne 'yan bindigan suka bude wuta kan fasinjoji, inda suka yi awon gaba da wasu tare da kashe wasu da dama, Daily Trust ta ruwaito.
A wani sabon rahoton da kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar kan aikin ceton da ake, ya ce yayin da aka gano gawarwaki takwas, mutane 26 da suka jikkata suna karbar magani.
Ya ce bisa ga bayanan da aka samu daga hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya, mutane 362 ne suka shiga jirgin.
Ripples Nigeria ta tattaro Aruwan na cewa::
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta samo cikakken bayanan fasinja daga Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC), na jirgin Abuja zuwa Kaduna AK9 wanda ‘yan ta’adda suka kai wa hari a ranar Litinin.
“A bisa ga takardun bayanan da aka samu, fasinjoji 398 ne suka sayi tikitin tafiya, amma 362 aka tabbatar da cewa sun shiga jirgin ta hanyar da aka sani.
“Bayanan na fasinja basu hada da ma’aikatan NRC da jami’an tsaro da ke cikin jirgin ba.
“Bugu da kari, hukumomin tsaro sun bayar da rahoton cewa an gano gawarwaki takwas sannan mutane 26 sun jikkata yayin harin.
"Har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano halin da fasinjojin da ke cikin jirgin ke ciki da har yanzu ba a san adadinsu ba a lokacin da aka samu wannan rahoton. Ana kuma ci gaba da gudanar da ayyukan bincike."
'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Hari Tashar Jirgin Kasa a Kaduna
A wani labarin, 'yan ta'adda sun kai hari tashan jirgin kasa na da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Channels Television ta ruwaito.
Majiyoyi sun ce yan ta'adda sun saka bam ne a kan layin dogon hakan ya tilasta wa jirgin da ya baro Abuja zuwa Kaduna ya dakata, Nigerian Tribune ta rahoto.
Wannan shine hari na biyu da yan ta'addan ke kai wa a hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.
Asali: Legit.ng