Yanzun Nan: IGP da COAS Sun nufi wurin da yan bindiga suka ɗana wa Jirgi Bam a Kaduna
- Shugaban yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, da shugaban Sojojin Najeriya, Janar Farouk Yahaya, zasu je wurin da yan bindiga suka dasa Bam
- Wannan na zuwa ne bayan wasu yan ta'adda sun dasa wa Jirgin ƙasa Bam, suka bude wa Fasinjoji wuta a layin Dogon Abuja-Kaduna
- Bayanai sun nuna maharan sun kashe wasu daga cikin Fasinjoji sun jikkata wasu, sannan suka tafi da wasu
Kaduna - Sufeta Janar na yan sandan ƙasar nan, Usman Alkali Baba, da shugaban rundunar Sojin ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, suna kan hanyar zuwa wurin da Bam ya tashi da jirgin ƙasa a Kaduna.
Manyan ƙusoshin tsaro biyu za su kai ziyara wurin ne domin duba yadda abun fashewan ya tashi da daren Litinin a layin dogon Abuja-Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yan bindigan da suka dasa Bam a kan hanyar jirgin sun zagaye shi bayan sun ta ɗa Bam ɗin kuma suka buɗe wa fasinjojin dake ciki wuta.
Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun kashe adadin mutane da ba'a gano ba har yanzu, yayin da wasu ke kwance a Asibiti da raunuka, kuma sun sace wasu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoto ya bayyana cewa tun da safiyar yau Talata, jami'an tsaro suka mamaye babbar hanyar Kaduna-Abuja domin tabbatar da tsaro.
Wata majiya daga cikin jami'an tsaro ta shaida wa manema labarai cewa ana tsammanin isowar COAS da IG zuwa jihar Kaduna da tsakar ranar nan ta yau.
Zasu haɗu da gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai a Rijana kuma daga nan zasu wuce kai tsaye zuwa wurin da lamarin ya faru.
"Tuni aka girke jami'an tsaro a yankin, hanyar tana lafiya lau," Majiya ɗaga jami'an tsaron ta tabbatar.
NRC ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ƙasa
A wani labarin kuma NRC ta dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna har ila ma sha'a Allahu
Hukumar sufurin jiragen kasa a Najeriya watau NRC ta sanar da dakatar da sufurin fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna har sai lokacin da hali yayi.
Wannan ya biyo bayan harin Bam da yan bindiga suka kaiwa jirgin daren Litinin a tsakanin garin Kateri da Rijana.
Asali: Legit.ng