Sakon kungiyar Izala ga Buhari: Bai kamata ka bari ASUU su ci gaba da yajin aiki ba

Sakon kungiyar Izala ga Buhari: Bai kamata ka bari ASUU su ci gaba da yajin aiki ba

  • Kungiyar addinin Islama a Najeriya, JIBWIS ta yi kira ga gaggauta shawo matsalar yajin aikin ASUU nan take
  • Kungiyar ta yi wannan kiran ne ta bakin shugaban majalisar malamai, Sheikh Sani Yahaya Jingir a jiya Lahadi
  • Hakazalika, Olubadan na yankin Yarbawa shi ma yayi irin wannan kira, inda yace ya kamata a warware yajin aikin cikin gaggawa

Jos, Filato - Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS), a ranar Lahadi, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su warware sabanin da ke tsakaninsu tare da janye yajin aikin malaman na jami'a.

Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya yi wannan kiran a wajen rufe taron karawa juna sani na kwanaki 29 na shirin watan Ramadan mai taken: “Shugabanci nagari da tsarin samar da tsaro ga jama’a” da aka gudanar a garin Jos.

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

Izala ta roki Buhari ya shawo kan matsalar yajin aiki
Sakon kungiyar Izala ga Buhari: Bai kamata ka bari ASUU su ci gaba da yajin aikin ba | Hoto: AlIrshaadTv
Asali: Facebook

Sheikh Jingir ya ce gwamnatin tarayya a nata bangaren ya kamata ta yi duk mai yiwuwa don ganin an warware matsalar da ke tsakaninta da ASUU domin kawo karshen yajin aikin.

Daily Trust ta rahoto Sheikh na cewa:

“Ba daidai ba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran masu ruwa da tsaki su yi shiru su bar yajin aikin ya ci gaba da tafiya. A matsayinka na shugaba idan mutane suka yi kuskure ka gyara su saboda Allah.
“Saboda haka, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da magance matsalolin da ke tsakaninta da ASUU domin baiwa dalibai damar komawa karatu.”

Ya kamata a shawo kan yajin aikin ASUU, Olubadan

A bangare guda, Olubadan na Ibadanland, Oba Lekan Balogun, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su sa baki a yajin aikin na ASUU da ke ci gaba da sanya dalibai zaman gida, domin ganin an shawo kan matsalar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

2023: Mulkin Buhari ba komai bane face yaudara, dan takarar shugaban kasa na PDP

Wani rahoton Vanguard ya naqalto Olubadan na cewa:

"A duk abin da muke yi a rayuwa, lokaci yana da mahimmanci kuma babu wata hanyar da za ta fanshe duk wani lokaci da aka bata, wannan yasa ya kamata dukkanin bangarorin da ke da hannu a cikin wannan batu su yi sulhu tare da kawo karshen shi saboda yara da iyayensu da abin ya shafa.”

Olubadan ya yi wannan roko ne a yayin ziyarar ban girma da shugabannin kungiyar tsofaffin daliban jami’o’in Najeriya (CAANU) karkashin jagorancin shugaban kungiyar Farfesa Ahmed Tijani Mora suka kai masa a fadarsa ta Alarere.

Ba wannan ne karon farko da sarakunan gargajiya da malaman addini da masu fada a ji a cikin al'umma ke kira ga shawo kan matsalar yajin aikin ASUU ba.

Gabanin zaben 2023: Tinubu ya ba jami'a kyautar N1bn ana tsaka da yajin aikin ASUU

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya baiwa jami’ar jihar Legas (LASU), gudunmawar kudi don gina wata cibiyar bunkasa ilimin jagoranci da ya kai Naira biliyan 1.

Kara karanta wannan

Jiragen Super Tucano sun yi lugude a maboyar ISWAP, Sani Shuwaram ya shura lahira, an nada sabon shugaba

Mataimakin shugaban jami'ar LASU, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello ne ya sanar da bayar da gudummawar a taron laccar yaye dalibai karo na 25 a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, mataimakin gwamnan jihar Legas Dr. Obafemi Hamzat ne ya wakilci Tinubu a wajen taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel