Da duminsa: Sojoji da ke sintiri a Sambisa sun samo ragowar jirgin NAF da yayi hatsari a 2021

Da duminsa: Sojoji da ke sintiri a Sambisa sun samo ragowar jirgin NAF da yayi hatsari a 2021

  • Rundunar sojin kasan Najeriya ta gano ragowar jirgin saman NAF da ya bace watanni 11 da suka shuɗe
  • Jirgin ya ɓace ne yayin da rundunar ke hanyar kaiwa sojin ƙasan Najeriya ɗauki a jihar Borno a shekarar da ta gabata
  • Yayin sanar da cigaban, rundunar ta sanar da yadda ta gano ragowar jirgin a lokacin da take sintiri a dajin Sambisa cikin Borno

Sambisa, Borno - Dakarun sojin kasan Najeriya na rundunar kakkabo hamada sun gano ragowar jirgin saman sojin saman Najeriya(NAF) da ya ɓace watanni 11 da suka shuɗe.

Rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter kan yadda jirgin saman Alpha Jet (NAF475) ya ɓace, yayin da yake kan hanyarshi ta kai gudunmawa ga sojin kasan Najeriya a Borno.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An yi artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram a Sambisa, Soji sun yi nasara

A lokacin, matuƙan jirgin har mutum biyu ne ke cikin jirgin.

Yayin bayyana cigaban a ranar Asabar, dakarun sojin sun bayyana yadda rundunar ta samu ragowar yayin da rundunar ke sintiri a dajin Sambisa a jihar Borno.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel