Sai ka kawo mahaifinka ko Malam Liman: Kotu ta ba da sharadin beli ga wanda ya kira Ganduje dan rashawa
- Wata kotu da ke zama a jihar Kano ta sake nazari kan sharuddan da aka bai wa Abdulmajid Kwaman da na beli
- A baya, kotu ta gindaya wasu sharudda masu tsauri ga mutum, wanda ake zargi ya ci mutuncin gwamna Ganduje
- A yanzu kuwa, kotun ta sake duba sharuddan, inda ta sassauta wasu bangarori domin ba da belinsa
Jihar Kano - A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke jihar Kano karkashin jagorancin Aminu Gabari, ta sake nazari kan sharuddan belin da ta sanya wa Abdulmajid Kwamanda a baya, bayan da lauyansa Tajuddeen Funsho ya roka masa sassauci.
Ana tuhumar Kwamanda ne da zargin kalaman batanci ga gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, inji rahoton Punch.
Lauya Funsho ya roki kotun da ta sake duba sharuddan belin da ta gindaya wa wanda yake karewa, inda kotu ta ce wanda ake kara zai ci gaba da zuwa kotu domin amsa tuhumar da ake masa.
Da yake mayar da martani, lauyan tsagin Ganduje, Ahmad Wada, ya ce batun duba sharuddan belin dai na hannun kotu, yana mai neman a yi amfani da sharuddan cikin adalci.
Meye hukuncin da Alkali ya yanke a zaman nan?
A hukuncin da kotun ta yanke, Alkali ya umarci Kwamanda da ya gabatar da wasu yardaddun mutane biyu wadanda suka hada da mahaifinsa ko waliyinsa maimakon Wakilin Gabas na masarautar Kano kamar yadda aka umarta a baya.
Kotun ta kuma umurci wanda ake kara da ya kawo Limami daga ko ma wane masallaci ne da ke unguwar Koki ko kuma wani masallacin da yake sallah..
Gabari ya kuma ce, wanda ake kara zai iya kawo ko ma wani irin shugaban addini ne a cikin al'umma idan ya kasa samun Limamin da zai tsaya masa.
Irin wannan malamin na addini da ya kawo zai maye gurbin babban Limamin masallacin Hajiya Mariya Sanusi Dantata da ke garin Koki, wanda kotu ta ce ya kawo a baya.
Kotun ta dage zamanta kan batun har zuwa ranar 19 ga Afrilu, 2022.
Dalilin gurfanar da Kwamanda
An gurfanar da wanda ake tuhuma ne a gaban kuliya bisa zarginsa da kalaman batanci kan gwamna Ganduje a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo.
Ya bayyana cewa gwamnan ya baiwa shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni cin hanci domin ya samu saukin amincewa da Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano.
An tasa keyar dan adawan Ganduje, Dan Bilki Kwamanda, gidan gyaran hali
Wata kotun majistare dake zamanta a unguwar Nomanland a cikin garin Kano ta tasa keyar wani dan adawar Gwamna Abdullahi Ganduje, Abdulmajid Danbilki Kwamanda.
An gurfanar da shi a kotu ne kan zargin batanci da sharri wa gwamna Ganduje, rahoton DailyTrust.
Rahotanni sun nuna cewa Danbilki ya zargi Ganduje da laifin bada cin hanci ga Mai Mala Buni da mambobin kwamitinsa don tabbatar da cewa Abdullahi Abbas, ya zama Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano.
Alkalin kotun, Aminu Magashi, a ranar Talata ya bada umurnin tasa keyar Kwamanda zuwa gidan yari bayan watsi da bukatar belin da lauyansa yayi.
Rikicin Kano: Sanata Shekarau ya caccaki Ganduje da APC, yace yanzu aka fara
A wani labarin, sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya nuna rashin jin dadinsa da kalaman gwamna Ganduje na murnar samun nasara a Kotu ranar Alhamis.
Premium Times ta rahoto cewa Shekarau ya zargi Ganduje da yin kalaman batanci ga mambobin tsaginsa a jawabinsa bayan hukuncin Kotu.
Kotun daukaka kara ta soke hukuncin babbar Kotun tarayya dake Abuja, wanda ya baiwa shugabannin APC na tsagin shekarau nasara.
Asali: Legit.ng