Akwai matsala: PDP ta gargadi INEC kan sanya ido da halartar taron gangamin APC
- Jam’iyyar PDP ta shawarci INEC da ta guji sanya ido kan abin da ta bayyana a matsayin taron gangamin APC wanda aka shirya ‘ba bisa ka’ida ba’
- Jam'iyyar adawan ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinta Debo Ologunagba ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris
- A cewar Ologunagba, INEC za ta saba wa ka’ida ta hanyar halartar taron gangamin da jam'iyyar mai mulki ta shirya
PDP ta gargadi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kada ta halarci taron gangamin jam’iyya mai mulki APC ko sanya ido kan lamurranta yayin tdaron.
Legit.ng ta tattaro cewa jam’iyyar PDP ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da kakakinta Debo Ologunagba ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.
Jam'iyyar adawar ta bayyana taron na ranar Asabar 26 ga watan Maris a matsayin taron hauragiya da jam'iyyar mai mulki ta shirya.
Ologunagba a cikin wata sanarwa da ya yada a shafin PDP na Facebook ya yi gargadin cewa hukumar zabe za ta fita daga dokokinta na kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar halarta ko kuma sanya ido a taron da APC ta shirya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
PDP ta yi zargin cewa APC ta daina fita bisa ka’ida tun bayan da ta rusa tsarukanta na kasa, jihohi da kananan hukumomi a ranar 8 ga Disamba, 2020 kuma ba ta iya bin dokokin INEC.
A bangare guda, PDP ta shawarci ‘yan Najeriya da ke da niyyar halartar taron da su nemi jagoranci, tare da lura da cewa suna tafiya ne da ba za su san inda za a je dasu ba.
Dalilin rabuwar kan sauran jam'iyyun siyasa: Babu jam'iyyar da ke da uba kamar Buhari, inji Ahmad Lawan
A wani labarin, sauran jam’iyyun siyasa a Najeriya “watakila” sun samu rabuwar kai ne saboda ba su da uba kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, wannan batu na zuwa ne daga bakin shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan bayan ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar gabanin babban taron gangamin jam’iyyar APC na kasa.
Lawan da yake magana a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, ya bayyana Buhari a matsayin uban da ke iya tabbatar da an sasanta tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, kuma kan kowa ya kasance a hade.
Asali: Legit.ng