Da Duminsa: Gwamna a Najeriya ya kori ma'aikata sama da 500 daga aiki, sun fantsama zanga-zanga
- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya amince da korar ma'aikata 513 daga bakin aiki waɗan da ke sashin harkokin wasanni
- A wani kundi mai ɗauke da sanarwan korar ma'aikatan, gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin domin garambawul ga sashin
- Ma'aikatan da korar ta shafa da suka haɗa da yan wasa da masu horarwa da shugabanni, sun fantsama tituna suna zanga-zanga ranar Laraba
Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya sallami ma'aikata 513 na sashin wasanni na jihar kuma matakin ya fara aiki tun daga Litinin 21 ga watan Maris, 2022.
Sallamar aikin a cewar rahoton Vanguard, na cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar 4 ga watan Maris, 2022, kuma waɗan da lamarin ya shafa ya kunshi manya da ƙananan ma'aikata.
Legit.ng Hausa ta gano gwamnatin na cewa matakin wani bangare ne na kokarin da take na canza salon sashin wasanni zuwa hukumar wasanni ta jihar Edo.
Zamu biya ma'aikatan da aka kora haƙƙinsu - Gwmanati
Sanarwan ta ƙara da cewa gwamnati zata biya ma'ikatan da korar ta shafa hakkokinsu na albashin wata ɗaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakanan ta ce za'a fara biyan ma'aikatan kuɗin Fanshon su a watan Afrilu, 2020, a rahoton Leadership ma'ikatan da aka sallama sun kai 514.
Ma'aikatan da matakin sallamar ya shafa sun haɗa da, yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle, masu horarwa da kuma na ɓangaren shugabanci.
Wane mataki ma'aikatan suka ɗauka?
A ranar 24 ga watan Maris, 2022, ma'aikatan da gwamnan ya kora suka fito gagarumar zanga-zanga a kewayen filin Samuel Ogbemudia da wasu tituna dake kusa.
Wasu daga cikin mutanen sun ce sun yi mamakin ganin sanarwan cewa an sallame su daga aiki, kuma aka ba su shawaran su sake neman aiki na wucin gadi.
Ɗaya daga cikin yan zanga-zangan, Patience Igbiti, ta ce:
"Sama da shekara 20 ina aiki a matsayin cikakkiyar ma'aikaciya kuma lokaci guda suka kore ni. Na ƙi karban ayyuka da dama a ƙasar waje domin na yi wa jihata aiki. Daga ina ake son na fara yanzu?"
Haka nan kuma wani ma'aikacin da lamarin ya shafa, Friday Aibangbe, ya ce:
"Ina da kwarin guiwar cewa gwamna bai damu da mu ba kwata-kwata. Mun masa aiki muka zaɓe shi kuma muka sadaukar domin shi, amma abin da ya saka mana da shi kenan yanzu."
Da yake jawabi ga masu zanga-zanga, shugaban hukumar wasanni, Yusuf Ali, ya ɗau alƙawarin kai korafinsu ga gwamnatin jiha.
A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kashe babban Basaraken gargajiya a Filato
Yan bindiga sun halaka Basaraken gargajiya a jihar Filato, yayin da yake kan hanyar zuwa gaida mara lafiya a Asibiti.
Wani mazaunin yankin ya ce tuni aka ɗakko gawarsa aka mata jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Asali: Legit.ng