Daukar fansa: Tsageru sun kone rugar makiyaya kurmus a yankin Kudancin Kaduna

Daukar fansa: Tsageru sun kone rugar makiyaya kurmus a yankin Kudancin Kaduna

  • Har yanzu ana ci gaba da rikici a yankin Kudancin Kaduna, inda wasu tsageru suka kone matsugunar Fulani
  • Wannan lamari na zuwa ne tun bayan da aka kai hare-hare wasu kauyukan yankin, tare da hallaka mutane da dama
  • Rahoto ya bayyana cewa, an samu mutanen da suka tada zanga-zanga tare da tada zaune tsaye a yankin

Kaduna - Wasu tsageru sun kona wasu rugagen makiyaya biyu a yankin Zauru da Kurdan a karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Rahoton The Nation ya ce, adadin wadanda suka mutu a hare-haren ranar Lahadi a Kaura da kuma zanga-zangar da ta biyo bayan rikicin Kafanchan ya kai 37, yayin da jami’an tsaro suka gano wasu gawarwaki uku a jiya.

Yadda tsageru suka kone rugagen Fulani a Kaduna
Rikicin: Wasu sun kone rugar Fulani kurmus a yankin Kudancin Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin tsageru

Kara karanta wannan

Karshen Mako: Yadda yan bindiga suka ɓarnata rayuka 62, sace wasu 62, suka kona gida 70 a Kaduna da Zamfara

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai a jihar ta Kaduna.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya bayyana cewa:

“Haren-haren tashin hankali ne wanda ba shi da gurbi a cikin al’umma masu wayewa. Hare-haren na farko da aka kai kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, jami’an tsaro da lalata gidaje da shaguna abu ne mai matukar zafi kuma abin Allah wadai.
"Al'ummar kasa na taya al'ummar Kagoto jimami, inda aka kai hare-haren da sojoji da suka rasa 'yan uwansu."

A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a jiya, ta ce shugaban karamar hukumar Zangon-Kataf, Francis Sani Zimbo ya gana da shugabannin gargajiya da na Kurdan da Zaurun domin kaucewa sabon rikci da ya biyo bayan kona rugagen makiyayan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Jaridar Punch ta rahoto Kwamishinan yana cewa:

“Hukumomin tsaro sun bayar da rahoton cewa sun gano gawarwakin wasu ‘yan kasa guda uku da wasu tsageru suka kashe a ranar Litinin a wurare biyu a kananan hukumomin Kaura da Jema’a.
“An gano gawar wani mutum mai suna Ibrahim Isiyaku (Danasabe) da ke zaune a lamba 143, titin Bauchi, Kafanchan."

Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana fita a Jema'a da Kaura a jiharsa

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita hana fita a kananan hukumomin Jema’a da Kaura biyo bayan samun bayanai na shawari daga hukumomin tsaro na jihar.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta shafinta na Twitter.

Sanarwar ta ce:

"Biyo bayan shawarwarin hukumomin tsaro, KDSG ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take. Hakan na nufin taimakawa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankunan, da ceton rayuka da dukiyoyi da kuma ba da damar maido da doka da oda."

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.