NDLEA ta kwace wiwi mai nauyin 374.397kg daga masu safara a jihar Kano
- NDLEA ta kwace wiwi mai nauyin kilo 374.397, tare da kama mutane 131 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a Kano, tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu, 2022
- Kwamandan NDLEA ya kara da bayyana yadda a watan Maris, hukumar ta lalata shuke-shuken wiwi, tare da damko mutane biyu a kananan hukumomi guda biyu na jihar
- Idris Ahmad ya bukaci mazauna jihar da su bada cikakkun bayanai game da sabgar da masu safarar miyagun kwayoyi ke yi a yankuna
Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), a jihar Kano ta bayyana yadda ta kama wiwi mai nauyin kilo 374.397, da wasu mutane 131, wadanda ake zargin su da safarar miyagun kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu, 2022.
Kwamandan NDLEA na jihar, Abubakar Idris Ahmad, ya bayyana hakan ne a Kano yayin wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba.
Ya ce, an damko wadanda ake zargin a wurare daban-daban a cikin jihar, bayan tsananta bincike da jami'an rundunar suka yi, inda ya kara da bayyana yadda wadanda ake zargin suka kunshi maza 125 da mata shida.
Kwamandan ya ce, hukumar ta kama wiwi mai nauyin kilo 374.397; Codeine mai nauyin kilo 1.3, Diazepam mai nauyin kilo 189.585, 100g na Raphenol da sauran haramtattun abubuwa cikin lokacin.
Ya kara da bada labarin yadda a cikin watan Maris, hukumar ta lalata shuke-sheken wiwi, gami da damko mutane biyu da take zargin a Bebeji da karamar hukumar Dawakin Kudu na jihar, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.
"Za mu cigaba da kewayawa duk wani lungu da sako na jihar don tabbatar da mun lalata duk wata gonar wiwi," a cewarsa.
Ya cigaba da bayyana yadda hukumar ba za tayi kasa a guiwa ba wajen yaki da ta'ammuli da miyagun kwayoyi, safararsu da sauran munanan ababe.
Idris Ahmad ya bukaci mazauna jihar da su bada cikakkun bayanai game da sabgar da masu safarar miyagun kwayoyi ke yi a yankuna.
Sannan ya bukaci iyaye da shugabannin yankin da su sa wa 'ya'yansu ido don tseratar da su daga ta'ammuli da miyagun kwayoyi.
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da 1.5m da za a kai Kebbi da Kano
A wani labari na daban, hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta kama kwayoyi akalla miliyan 1.5 na magunguna irin su Tramadol, Exol-5 da Diazepam da aka loda a Onitsha, jihar Anambra.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, a Abuja, Vanguard ta rahoto.
Mista Babafemi ya ce, magungunan da ke kan hanyar zuwa Yauri a jihar Kebbi, hukumar NDLEA ce ta kama su a Edo, a ranar Juma’a 14 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng