Ba Mu Son Jin Dogon Labari, Ka Bamu Wutar Lantarki Kawai, Majalisa Ga Ministan Makamashi
- Jiya kwamitin wutar lantarki na majalisar wakilai, ta titsiye ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu akan kin tsayawa ya yi bayani dangane da rashin wutar da ake fama da shi
- A cewar ‘yan majalisar, ba sa da bukatar ya karanta musu dogon labari kawai so suke yi ya sanar da su amsoshi da kuma mafita dangane da halin rashin wutar da Najeriya take fuskanta
- ‘Yan majalisar sun gayyaci ministan ne don ya sanar da su abin da ke faruwa, saboda a cewar kwamitin, ‘yan Najeriya sun shiga damuwa kuma matsalar rashin wuta ta taba sana’o’in su
Abuja - Kwamitin wutar lantarki ta majalisar wakila, ta turke ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, inda ta dakatar da shi daga karanto labari ko kuma surutai marasa amfani, Vanguard ta ruwaito.
A cewar kwamitin, tana bukatar amsoshi ne kadai da kuma mafita dangane da matsalar wutar lantarkin da Najeriya take fuskanta a halin yanzu.
Shugaban kwamitin, Honarabul Magaji Aliyu, yayin jawabin sa na bude taron ya sanar da ministan cewa ‘yan Najeriya suna cikin damuwa kasancewar yadda rashin wutar nan ya taba sana’o’in su.
Kamar yadda ya bayyana:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Idan za a tuna da kyau, ‘yan Najeriyan da muke wakilta suna kan fuskantar mawuyacin yanayi na matsalar wuta wanda ya fi ko wanne muni a fadin kasar nan. Wannan ya janyo wa mutane matsaloli na rashin walwala da jin dadi.
“Ya lalata kananun sana’o’in jama’a wadanda suka dogara da wutar lantarki. Sannan ya kawo cikas ga harkokin da ke bukatar wutar. Ga zafin da ake ciki wanda ya janyo rashin walwala ga mutane.”
Ministan ya fara bayani akan nasarorin ma’aikatar wanda ya sa ‘yan majalisar suka yi ca akan ta
Ya ci gaba da cewa, hakan yasa suka gayyace shi don ya bayyana musu menene matsalar, kuma ya za a yi wurin samar da mafita?
Yayin bayar da amsa dangane da tambayoyin kamar yadda Vanguard ta nuna, ministan wanda ya samu wakilcin sakataren ma’aikatar, Mr. Nebolisa Anako, ya dauki zungureriyar takarda wacce ciki ya fara lissafo tarin nasarorin da ma’aikatar ta samu, wanda hakan bai kayatar da ‘yan majalisar ba.
Bayan fara sauraro ne suka dakatar da shi, inda suka ce kawai amsoshi suke so ya ba su dangane da rashin wutar da kasa take fama da shi ba dogon labari ko kuma karatu ba.
“Ministan yana ba mu bayani dangane da yadda aka samar da wuta, ba ma bukatar jin wasu surutai, kawai so muke yi mu ji musababbin rashin wutar lantarki a kasar nan da kuma hanyar magance ta,” inji Injiniya Mohammed Wudil, dan majalisa mai wakiltar mazabar Wudil da ke Kano.
‘Yan majalisar sun bukaci sanin lokacin da za a kawo karshen matsalar
Hon. Aisha Dukku daga Jihar Gombe ta kada baki ta ce:
“Me sakatare yake son fada mana? Yana nufin za mu ci gaba da zama cikin duhu kenan har karshen 2023? Haba! A’a!”
Muraino Ajibola daga Jihar Oyo ya ce:
“Ba yanzu aka fara samun wannan matsalar ba. Kusan duk shekara sai an samu matsalar rashin wuta tsakanin watan Janairu zuwa Maris. Muna da isasshen sinadarin gas. Yanzu a takaita bayani, ba a shirya bayar da wuta bane ko kuma me? A kirga mana nawa gyaran zai ci?”
Sauran ‘yan majalisa sun dinga caccaka da nuna rashin amincewar su dangane da halin da kasa take ciki. Sun bukaci a yi gaggawar kawo mafita.
Shugaban kwamitin ya nemi ministan ya je ya kuma dawo da mafita akan matsalolin
Shugaban kwamitin, Honarabul Aliyu ya ce majalisar za ta tabbatar an maido da kamfanin siyar da wutar lantarki, NBET ga ma’aikatar wutar lantarkin.
Ya kuma bukaci ministan ya je ya kuma dawo ranar Juma’a da mafita dangane da matsalolin wutar lantarkin da Najeriya ta ke fuskanta.
Asali: Legit.ng