Haba N1k: Yiwa direban NAPEP kyautar N1k bayan dawo da wayoyi 10 da ya tsinta ya bar baya da kura

Haba N1k: Yiwa direban NAPEP kyautar N1k bayan dawo da wayoyi 10 da ya tsinta ya bar baya da kura

  • Gaskiyar wani direban keke napep ya narkar da zukatan jama'a a shafukan sada zumunta tare da sanya jama'a cikin mamaki
  • Direban dan Najeriya ya gano cewa wani fasinja ya manta wata jaka dauke da sabbin wayoyi guda 10 a cikin kekensa, inda ya yi kokarin gano mai shi
  • A wani faifan bidiyo da ke zagayawa a intanet, a karshe ya gano mai jakar kuma an ba shi kyautar N1k kadai

Wani fasinja ya cika da mamaki bayan da wani abin da ya manta a cikin keken napep ya dawo hannunsa sanadiyyar direban keke napep mai kyawun zuciya.

Wani shafin Instagram @gossipmilltv ya watsa wani faifan bidiyo da ke nuna lokacin da direban keken ya gano mai jakar da ke dauke da sabbin wayoyi guda 10 da sauran kayayyakin da ya manta lokacin da ya hau kekensa.

Kara karanta wannan

TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido

Yadda mai NAPEP ya samu alherin 1k
Haba N1k: Yiwa direban NAPEP kyautar N1k bayan dawo da wayoyi 10 da ya tsinta ya bar baya da kura | Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

A cewar direban mai gaskiya, ya yi kokarin gano mai kayan ne bayan da ya gano jakar mai dauke da kayayyaki a cikin abin hawansa.

A karshe ya yi nasara da bincikensa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon:

Direban ya samu kyautar kudi

Yayin da ‘yan kallo suka yaba masa da ya mayar da kayan da ba nasa ba, direban cikin murmushi ya ce duk da cewa shi mashayin giya ne, sata abu ne da ba zai taba yi ba.

Legit.ng ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Aba na jihar Abia.

An ce an baiwa direban kyautar N1k ne kadai saboda gaskiyarsa.

Martanin 'yan soshiyal midiya

@hype_frosh ya ce:

“Shima mutumin bai da kudi, abun da yake da shi shine dubu daya idan yana da abun da ya fi hakan zai basa don nuna godiya kan dawo da wayoyi da ya yi, dan uwa Allah ya shi maka albarka.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

@cruiseloadedblog ya ce:

“Dukkan ku masu cewa dubu daya idan mutumin bai da abun da ya fi dubu daya sai ya kashe kansa, duk yakamata ku koyi yadda ake alkhairi ba tare da sa ran samun tukwici ba.

@queenseyyxo said:

"Nasan zai koma gida ya yi kwanaki 40 babu bacci yana mamakin dalilin da yasa ya dawo da wayoyi masu kyau a ranar."

@temmiehairlyn ya ce:

"Amma ba shi 1k ya danyi wani banbarakwai haka':…………. Kuma ka manta wayoyi guda 10, ba ka kyauta ba oooo."

Yadda saurayi mai shekara 18 ya zama Ango, ya auri ‘Yar shekara 16 a jihar Bauchi

A wani labarin, a ranar Juma’ar da ta gabata, aka ga wani aure da ba kasafai aka saba daura irinsa ba, saboda rashin yawan shekarun amaryar da angonta.

Daily Reality ta ce a kauyen Tilden Fulani, karamar hukumar Toro, jihar Bauchi, Muhammad Ahmad Salihu ya auri Amaryarsa Sumayyah Adam Ibrahim.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Majiya ta shaidawa jaridar cewa shekarun wannan Bawan Allah Muhammad Ahmad Salihu 18 a Duniya, ita kuma Sumayyah Adam Ibrahim ta na 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.