Yadda saurayi mai shekara 18 ya zama Ango, ya auri ‘Yar shekara 16 a jihar Bauchi

Yadda saurayi mai shekara 18 ya zama Ango, ya auri ‘Yar shekara 16 a jihar Bauchi

  • A makon da ya wuce ne wani ‘Dan shekara 18 ya shiga daga ciki a wani kauye a Arewa maso gabas
  • Malam Muhammad Ahmad Salihu ya auri Sumayyah Adam Ibrahim ‘yar shekara 16 rak a Duniya
  • An daura wannan auren da ya jawo surutu ne a kauyen Tilden Bauchi, garin Toro, a jihar Bauchi

Bauchi - A ranar Juma’ar da ta gabata, aka ga wani aure da ba kasafai aka saba daura irinsa ba, saboda rashin yawan shekarun amaryar da angonta.

Daily Reality ta ce a kauyen Tilden Fulani, karamar hukumar Toro, jihar Bauchi, Muhammad Ahmad Salihu ya auri Amaryarsa Sumayyah Adam Ibrahim.

Majiya ta shaidawa jaridar cewa shekarun wannan Bawan Allah Muhammad Ahmad Salihu 18 a Duniya, ita kuma Sumayyah Adam Ibrahim ta na 16.

An daura auren ne a babban masallacin kungiyar Ahlussunnah Wal Jama’a Izala da ke Tilde.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 8 da Hukumar Kwastam ta hana fitar da su zuwa kasashen waje

Auren wuri a Arewa

Mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu a game da auren. Kamar yadda mu ka samu labari, an yi bikin auren lafiya ba tare da an samu wata matsala ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kasar Arewacin Najeriya inda ake da yawan Hausawa da Fulani, ba abin mamaki ba ne a ga saurayi ko budurwa tayi aure a irin wadannan shekaru.

Sabon Ango a Bauchi
Sabon Ango Muhammad Ahmad Salihu Hoto: dailyrealityng.com
Asali: UGC

Wasu su na ganin wadannan Bayin Allah ba su isa su rike kansu ba. A daidai wannan lokaci, wasu su na ganin babu matsala idan har an iya dafa masu.

Wani malami a jami’ar Bayero da ke garin Kano ya bayyana cewa babu laifi yin hakan, ya yi masu addu’a, tare da kira ga iyayensu da su yi masu jagoranci.

Tir da wannan auren

Shi kuma Ya’u Sule Tariwa ya soki wannan aure da aka daura, ya ce sam ba abin burgewa ba ne.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

“Ban ga abin burgewa a nan ba. Iyayen yaran nan su maida hankali a kan cigaban rayuwarsa ba aure ba. Shekararsa 18 fa kacal! Haba!”

- Ya’u Sule Tariwa

Tuni mutane suka shiga maida masa martani a shafinsa na Facebook, su na cewa hakan ba laifi ba ne idan iyanesa su na da hali, kuma yin hakan sutura ne.

Hakan daidai ne

Legit.ng Hausa tayi magana da wani dalibin ilmi, Malam Ibrahim El-Caleel wanda ya bayyana cewa babu matsala a game da wannan auren da aka daura.

Ibrahim El-Caleel ya ce an saba jin budurwa tayi aure ta na shekara 16. Sannan shi kan shi Angon ya kai munzalin da zai zauna da ‘diya mace a karkashinsa.

A cewarsa Duniya ta canza ko ta ina, yara tun su na kanana sun san inda aka dosa. Ganin yadda lalata ta yawaita a zamanin yau, yin auren abu ne mai kyau.

Kara karanta wannan

Rashin wuta, wahalar mai, ASUU da matsin lamba 6 da ‘Yan Najeriya suka shiga ciki a yau

Asali: Legit.ng

Online view pixel