Halin da kasa ke ciki: Ortom ya shawarci Buhari da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga Osinbajo

Halin da kasa ke ciki: Ortom ya shawarci Buhari da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga Osinbajo

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya magantu a kan halin da kasar nan ke ciki a yanzu
  • Ortom ya shawarci shugaban kasa Buhari da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga Osinbajo
  • Sai dai ya ce ba wai yana sukar gwamnatin Buhari bane kawai illa cewa yana hakan ne saboda kishin kasa da gaskiya

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan jefa Najeriya a rikicin tattalin arziki da kuma gazawarsa wajen magance matsalolin tsaro a kasar.

Ortom ya yi kira ga shugaban kasar da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Halin da kasa ke ciki: Ortom ya shawarci Buhari da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga Osinbajo
Halin da kasa ke ciki: Ortom ya shawarci Buhari da ya yi murabus sannan ya mika mulki ga Osinbajo Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A wata hira da Sunday Vanguard, Ortom ya kuma ce goyon bayan shugaba Buhari da ya yi don ya zama shugaban kasa a 2015 kuskure ne.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Ɗaure Wani Ɗalibi a Gidan Yari Saboda Ya Saci Taliya Da Indomi

Ya kuma jadadda cewar sukar da ya yiwa gwamnatin tarayya karkashin APC ya samo asali ne daga kishin kasa, daidaito, adalci da kuma gaskiya.

Ortom ya ce:

“Gwamnatin tarayya ta gaza gaba daya, ko shakka babu, kuma ina so nay i kira ga shugaban kasa Buhari da ya yarda da cewar ya gazawa kasar nan kuma ina so na bashi shawara da ya yi murabus daga matsayin shugaban Najeriya cikin mutunci sannan ya mika mulki ga mataimakinsa domin ya jagoranci harkokin kasar nan. Idan bah aka ba, kasar nan za ta je kasa.
“Na ji takaici matuka kuma wannan ne dalilin da yasa nake kira ga shugaban kasar da ya yi murabus saboda ba zai iya jagoranci da magance halin wahala da yan Najeriya ke ciki ba. Ina kira gare shi da ya yi murabus. Shugaban kasar ya yarda da hakan sannan ya kira dukkanmu ba tare da la’akari da siyasa da addini ba, sannan ya fada mana gaskiyar abun da ke faruwa. Idan yana son ya karbi shawararmu, abubuwa za su koma kan hanya. A shirye muke mu hada kai mu yi aiki da shi.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Abin da Buhari yace da na fada masa inason na gaje shi, Tinubu ya magantu

Kan rawar da ya taka wajen ganin Buhari ya zama shugaban kasa a 2015, da dalilin da yasa alakarsu ta yi tsami, tsohon ministan ya ce kuskure ne.

Vanguard ta kuma nakalto Ortom yana fadin:

“Eh ina daga cikin wadanda suka yi aiki don zaben shugaban kasa a 2015. Mun jajirce saboda alkawaran da ya yi mana. Ya bamu tabbacin cewa zai zamo shugaban kasa na kowa ba na wani ba amma a yau, karara mun ga cewa shugaban kasa shugaba ne na Fulani.
“Tun bayan da Najeriya ta samu ‘yancin kai, ba mu taba ganin irin wannan son zuciya da ke gudana a kasarmu ba. Ba mu taba ganin irin wannan rashin hadin kai da rashin tsaro a kasar nan ba. Ba mu taba ganin irin wannan koma bayan tattalin arziki kamar yadda muke da shi a yau ba. Maganar ta shafi rashin kwarewa, rashin iya aiki, da kuma rashin hangen nesa da alkiblar jagorancin kasarmu. Don haka, kawai mun yi kuskure ne a 2015 amma cikin ikon Allah jam’iyyar PDP a shirye take ta kwato mana kasarmu ta sake gina ta, ta kuma dauke ta daga kasa zuwa sama.”

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

Kan rashin tsaro, Ortom yay i bayanin cewa babban hakkin kowani gwamnati shine samar da tsaron rayuka da dukiyoyi. A cewarsa:
“Matakin da rashin tsaro ya kai a kasar a yau abun damuwa ne. Na sha yin magana game da tarurrukan tsaro. Ba wai kawai ina suka bane illa ina son samar da mafita ga matsalolin da muke da su. Idan ka kira mu ga taron tsaro sannan ka kasance mai fadin gaskiya, za mu shawarce ka sannan mu hada kai mu kuma fito da mafita.”

Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace

A wani labari na daban, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fahimci yadda ake tafiyar da shugabancin zamani ba.

Tambuwal a ranar Asabar, 19 ga watan Maris, ya ce alakar da ke tsakanin shugaban kasar da Najeriya tamkar ‘auren dole’ ne, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ubandoma: Atiku bai taba tafiyar neman lafiya Turai a boye ba

Da yake magana a sakatariyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kaduna, gwamnan na jihar Sokoto ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da lalata kasar, Thisday ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng