Buhari Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya Kan Ƙarancin Man Fetur Da Rashin Wutar Lantarki
- Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi afuwar yan Najeriya bisa wahalhalun da suka shiga saboda karancin man fetur da daukewar wutar lankarki a kasar.
- Shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa gwamnati na aiki dare da rana don magance matsalolin kuma a halin yanzu an fara samun sauki a wasu jihohin kasar
- Buhari ya kuma bayyana cewa ya samu rahoton cewa akwai wasu mutane cikin masu gidan mai da wurin dakon mai da ke kawo cikas kuma ya ce a dauki mataki a kansu
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bawa yan Najeriya hakuri bisa daukewar wutar lantarki a kasa baki daya da kuma karancin man fetur da ya jefa yan kasar cikin wahalhalu masu yawa, rahoton Vanguard.
Shugaban kasar cikin wata sanarwa da hadiminsa Garba Shehu ya fitar ya nuna rashin jin dadinsa bisa mawuyacin halin da yan Najeriya suka shiga ciki sakamakon matsalolin.
A cewar shugaban kasar, 'gwamnati ta san cewa karancin man fetur din ya jefa yan kasa cikin mawuyacin hali kuma ya shafi kasuwancinsu, amma sauki na nan tafe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ina neman afuwar dukkan al'ummar kasa saboda wannan. Gwamnati na aiki dare da rana don magance matsalar. An aiwatar da tsari don magance karancin man fetur. Muna aiki tare da kungiyar manyan dillalan man fetur, MOMAN, da kungiyar dillalan fetur masu zaman kansu, IPMAN, kuma haka ya fara cimma ruwa.
"An samu isashen man fetur a wasu jihohi, duk da layi a gidajen mai. A cikin yan kwanakin nan, muna sa ran sauran jihohin su samu man.
"An tanadi kudi domin tabbatar da mai a kasar don gaba. Farashin makamashi ya tashi a kasuwan duniya a baya-bayan nan, amma gwamnati za ta tabbatar hakan bai shafi yan Najeriya ba."
Buhari ya bada umurnin a dauki tsatsaurin mataki kan masu hana ruwa guda a bangaren samar da fetur
Ya ce ya samu bayanai da ke nuna wasu mutane a wurin dakon man feur da kuma cikin masu gidajen mai suna aikatawa abubuwan da ka iya tsananta matsalar, rahoton Daily Trust.
A game da hakan, Shugaban kasar ya umurci Ma'aikatar Albarkatun Man Fetur, Da Hukumomin Da Ke Kula da Harkokin Man Fetur da NNPC da sauran hukumomin tsaro su dauki tsatsauran mataki a kansu.
Buhari ya kuma ce:
"Ana daukan mataki kan daukewa wutar lantarki. Hakan ya faru ne sakamakon karancin lantarki da aka samu daga tashohin lantarkin saboda sauyin yanayi tare da wasu matsaloli. A kan hakan, gwamnati na kokarin ganin kawo karshen matsalar don a cigaba da samun isashen lantarki."
Buhari ya bada tabbacin cewa za a samu biyan bukata nan bada dadewa ba saboda jajircewar da gwamnati ke yi don magance matsalar.
Farashin lantarki ya tashi bayan Gwamnati ta yi wuf, ta dakatar da tallafin wuta
A wani labarin, Hukumar Nigerian Electricity Regulatory Commission mai kula da harkar wutar lantarki a Najeriya ta ce gwamnatin tarayya ta janye tallafin wuta.
Punch ta rahoto hukumar NERC a ranar Laraba ta na cewa tallafin shan wutan da ya ci wa gwamnatin tarayya N600bn ya zo karshe a halin yanzu.
NERC ta bada sanarwar kara farashin shan wutar lantarki a Fubrairun wannan shekara ta 2022. An dauki wannan mataki ba tare da wani bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng