Sun ji wuta: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun kashe da yawa, wasu sun tsere

Sun ji wuta: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun kashe da yawa, wasu sun tsere

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar ragargazar wasu 'yan bindiga a yankin jihar Benue a jiya Talata 15 ga watan Maris
  • Wannan hari dai ya jawo martanin shugaban 'yan bindigan yankin, inda ya ce sai ya dauki fansa fiye da abin da aka yi masa
  • Ya zuwa yanzu, rahotanni sun ce an samu nasarar hallaka 'yan bindiga hudu, kuma an kwato kayayyaki` da yawa

Jihar Benue - Rahoton da Daily Trust ta fitar ya ce, an harbe wasu daga cikin ‘yan bindiga da ke barna a karamar hukumar Kastina-Ala ta jihar Benue.

A kalla hudu daga cikin ‘yan ta’addan ne sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) da ke aiki na musamman a Benue suka kashe.

Yadda sojoji suka hallaka 'yan bindiga a Benue
Sun ji wuta: Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun kashe da yawa, wasu sun tsere | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka hallaka 'yan sanda da dama a Kebbi

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Kastina-Ala, Alfred Atera, ya shaida cewa, shugaban ‘yan bindigan, Terna Gide, ya yi barazanar kai hari kauyukan da ke kusa da shi, inda aka kashe mutanensa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atera ya ce:

“Bayan harin da ‘yan tawagar ta OPWS suka kai a sansanin Tse-Keji a jiya (Talata) inda aka kashe hudu daga cikin ‘yan bindigan, an lalata musu sansaninsu tare da tattara wasu layu, Terna Gide na barazanar daukar fansa.
“Tun safiyar yau (Laraba), ya kira (Terna) ya yi barazanar cewa zai yi fiye da abin da aka lalata a sansaninsa. Ya kira daya daga cikin masu gadin sa kai na yankin ta waya domin ya fadi wannan barazanar.”

Hakazalika, wata majiyar sojan da ta ki yarda a ambaci sunanta, ta shaida wa Daily Trust cewa, ‘yan tawagar ta OPWS sun gudanar da atisaye a yankin da lamarin ya shafa tare da hallaka 'yan bindiga guda hudu.

Kara karanta wannan

Rikici: An kaure tsakanin sojoji da wasu matasa, an hallaka mutane akalla 6

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“A jiya (Talata) sojojinmu da ke Gbise da ke Kastina-Ala sun gudanar da rangadin share fage har sai da suka ci karo da ‘yan bindiga a Tse-Keji, an yi musayar wuta amma sojojinmu sun ci karfinsu.
“Saboda haka, ‘yan bindigar da ke dauke da makamai sun gudu cikin daji cikin rudewa amma sojojinmu sun fatattake su, kuma an kashe ‘yan bindiga hudu. An gudanar da bincike a maboyar inda sojoji suka kona sansanin baki daya.

Abubuwan da aka kwato

Majiyar ta soji ta ce an gano kayayyaki da yawa daga sansanin 'yan ta'addan. Legit.ng Hausa ta hada abubuwan kamar haka:

  1. Zagaye 9 na harsasan masu girma 7.6mm na musamman
  2. Ganga daya na bindigar dane,
  3. babura biyu
  4. Wayoyin hannu
  5. akunkuna na tabar wiwi
  6. Jimlar KUDI Naira 57,390
  7. Manyan layu iri-iri

Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14

Kara karanta wannan

An yaye tubabbun yan ta'addan Boko Haram 500 da aka yiwa horo

A wani labarin, rundunar tsaro ta NSCDC, reshen Jihar Kano, ta samu nasarar damkar wani Ahmad Abdulsalam da tsakar daren Talata da katinan waya guda 22 duk masu rijista da kuma wasu katin mutane daban-daban na banki guda 14.

Kwamandan rundunar, Adamu Zakari, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata da dare cikin garin Kano, The Punch ta ruwaito.

Ya kwatanta kamen a matsayin nasara mai yawa cikin kankanin lokaci daga hawan sa mukamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.