Yanzu-yanzu: Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a cikin kotu

Yanzu-yanzu: Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta fadi a cikin kotu

Abuja - Ramatu Kyari, Matar jami'in dan sandan Najeriya da aka dakatar, DCP Abba Kyari, ta yanke jiki ta fadi cikin harabar babbar kotun tarayya dake birnin Abuja.

Matar, sanya da bakin Hijabi ta yanke jiki ta fadi ne lokacin da Alkali Emeka Nwite yayi watsi da bukatar belin Abba Kyari bisa zargin safarar hodar iblis da ake masa.

Matar ta zube kasa ne lokacin da jami'an NDLEA suka tasa keyar Abba Kyari da sauran wadanda ake zargi daga cikin kotun, rahoton Vanguard.

Kamar ta sume, wasu jami'an NDLEA da lauyoyi sukayi gaggawan kwasheta daga kasa kuma suka shigar da ita daya daga cikin ofishohin dake cikin kotu.

Kawo yanzu misalin karfe 11, ana kokarin nema mata abin shaka lokacin da matan da suka rako ta kotu suke cewa tana fama da cutar asma.

Kara karanta wannan

Tserewa zai yi: NDLEA ta ki amincewa da bukatar belin Abba Kyari, an dage kara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng