Abin al'ajabi: Labarin Baturiyar da ta shekara 30 tana karantar da Hausa a Najeriya

Abin al'ajabi: Labarin Baturiyar da ta shekara 30 tana karantar da Hausa a Najeriya

  • Wata baturiya da ta shigo, ta rayu kuma ta yi aiki a Najeriya da sunan wa’azin mishan tsawon shekaru 30 ta cika shekaru 80, kamar yadda danta ya sanar
  • Matar mai suna Frances Boer ta yi aiki a jihohin Taraba da Filato inda ta kasance malamar firamare kuma mai koyar da harshen Hausa
  • Dan nata, Wiebe Boer ya saka hotunan a LinkedIn, inda ya nuna mahaifiyar tasa a lokacin da take aiki a Najeriya a matsayin malamar makaranta

Wata mata ‘yar kasar Holland da ta yi aikin wa’azin addinin kirista a Najeriya na tsawon shekaru 30, ta cika shekara 80 da haihuwa.

Abin da zai ba ku mamaki shine, matar mai suna Frances Boer ta yi aiki a yankin Arewacin Najeriya inda ta yi aiki a makarantun firamare tare da koyar da harshen Hausa.

Kara karanta wannan

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

Baturiya ta ba da mamaki sadda take koyar da Hausa
Ta musamman: Labarin Baturiyar da ta shekara 30 tana karantar da Hausa a Najeriya | Hoto: LinkedIn/Wiebe Boer
Asali: UGC

Frances Boer 'yar kasar Holland ce

An haifi Frances a kasar Holland a lokacin yakin duniya na biyu amma daga baya ta yi hijira zuwa Amurka sannan ta dawo Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake yada hotunan, danta ya rubuta shafin LinkedIn cewa:

"Ina taya ki murnar cika shekaru 80 mahaifiya, FRANCES BOER. An haife ta a Friesland (Netherland) da aka mamaye a lokacin yakin duniya na biyu, ta yi hijira zuwa Amurka tare da iyayenta da yayyenta shida lokacin tana da shekaru 6, sannan tana shekaru 24 ta koma Najeriya inda ta yi aikin wa’azi mishan na kasashen waje a Taraba da Filato na tsawon shekara 30 tare da mahaifina. Yanzu ta yi ritaya a Vancouver, Kanada.
"Lokacin a Najeriya ta kasance edita, malamar makarantar firamare kuma malamar harshen Hausa ga 'yan Najeriya da 'yan kasashen waje."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Game da yadda ta koyi harshen Hausa har ta kai ga koyar dashi ga dalibai, Boer ya ce:

“Mahaifina da mahaifiyata sun karanci Hausa a Jami’ar Jihar Michigan na tsawon shekara daya kafin su tafi Najeriya a 1966, sannan kuma shekaru goma na farkonsu a Najeriya sun kasance a Wukari da Baissa a Taraba inda dole suka yi ta magana da Hausa don haka dukkansu suka kware sosai.
"A shekarun 1980 mahaifiyata ta kasance tana koyar da ’yan Najeriya harshen Hausa, kuma mahaifina yana rubuta littattafai da harshen Hausa.”

Martanin 'yan sohiyal midiya

Bayan Boer ya ba da labarin mahaifiyarsa, mutane da yawa sun ji sha'awar labarin, kuma sun fara bayyana ra'ayoyinsu.

Ga kadan daga cikin abubuwan da suke cewa:

Sylvester Oluoha ya ce:

"Wannan kyakkyawan abu ne Wiebe Boer, Ph.D. Na tabbata ta sanya maka sunan Hausawa... Menene sunanka na Hausa?"

Christabel Bentu ya ce:

"Mama barka da zagayowar ranar haihuwa...ki godewa Allah da shekaru da yawa da kika yi da kuma shekaru masu yawa da za ki yi a gaba..."

Kara karanta wannan

Wani hanin: Bayan shekaru 12 tana dako, Allah ya azurta mata da haihuwar 'ya'ya hudu nan take

Zan hadu da rabo na: Mai digirin da ke tallan 'yan kamfai ya ce bai fidda rai da yin arziki ba

A wani labarin, wani matashi, Charles Ifeco, mai sayar da ’yan kamfai a baro ya yada wani bidiyonsa mai ban sha’awa a yanar gizo yayin da ya zaburar da mutane kan a kama sana'a.

A cikin gajeren faifan bidiyon, matashin ya nuna irin kokarinsa na neman kudi, inda ya nuna kalan kayan da yake sayarwa ba tare da nuna kin sana'ar ba, kana yake fatan samun canji.

A faifan bidiyo da aka yada a shafin Instagram, Charles ya shiga gaban kamera, yana tambayar mutane ko suna jira su ga yadda rayuwa za ta sauya masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.