Tafiyar Buhari Landan: Har yanzu shuru, Buhari bai sanar da Majalisa ya mika mulki ga Osinbajo ba
- Har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanar da majalisar dokokin kasar batun mikawa mataimakinsa, Yemi Osinbajo mulki ba a hukumance
- A yayin zaman majalisar na ranar Talata, 8 ga watan Maris, wanda shine na farko bayan tafiyar tasa, ba a ji an karanto kowani wasika kan haka ba
- Wani jami'in hulda da jama'a na majalisar ya tabbatar da cewar babu wata takarda da ta fito daga fadar shugaban kasa kan tafiyar Buharin
Duk da cewar da ya yi mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai ci gaba da gudanar da harkokin Najeriya a yayin tafiyarsa Landan jinya, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanar da majalisar dokokin kasar batun mika mulkin ba a hukumance, The Punch ta rahoto.
A zaman majalisar dokoki da aka yi na ranar Talata, wanda shine na farko bayan tafiyar Buhari, ba a ji shugabannin majalisun sun karanto kowani wasika daga shugaban kasar game da mika mulkin ba.
Rahoton ya nuna cewa da aka tuntube shi domin tabbatar da ko fadar shugaban kasa ta sanar da majalisar batun tafiyar Buharin, wani jami’in daya daga cikin ofisoshin hulda na majalisar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce “babu.”
A ranar Lahadi shugaban kasar ya ce Osinbajo zai kula da mulkin kasar yayin da shi zai kasance a Landan na tsawon makonni biyu don duba lafiyarsa.
Buhari ya fadi hakan ne kafin jirginsa ya tashi daga filin jirgin saman na Nnamdi Azikiwe, Abuja, da misalin karfe 2:00 na ranar Lahadi.
Ya ce:
“Ba zan yi ikirarin yin komai ni kadai ba. Gwamnati ta na nan. Mataimakin shugaban kasa ya na nan. A dokar kasa, idan ba na nan, to shi ne rike da kasa.”
“Kuma mu na da sakataren gwamnatin tarayya (Boss Mustafa) da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa (Ibrahim Gambari), don haka babu matsala.”
Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda zai iya magance matsalar tsaro a Najeriya
A wani labarin, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa domin tunkarar kalubalen tsaro a Najeriya yadda ya kamata, kasar na bukatar shugabanni irin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Asabar, 5 ga watan Maris, a jihar Delta, inda ya kai ziyarar ban girma ga Ovie na masarautar Uvwie, HRM Dr. Emmanuel Ekemejewan Sideso; da Olu na Warri, HRM Ògíamɛ̀ Atúwàtse III, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya kuma kara da cewa gwamnatoci kadan ne suka fuskanci kalubalen tsaro irin wadanda suka dabaibaye Najeriya a halin yanzu kafin Buhari ya hau mulki a 2015.
Asali: Legit.ng