Jami'an tsaro sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane bayan sace matar aure a jigawa

Jami'an tsaro sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane bayan sace matar aure a jigawa

  • Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta kama wani mutum da ake zargin kasurgumin mai garkuwa da mutane ne
  • Rundunar 'yan sandan ta bayyana yadda jami'anta suka yi aiki da bayanin sirri wajen tabbatar da kama mutumin
  • Ya zuwa yanzu, an ce ana ci gaba da bincike don tabbatar da gaskiyar lamari kafin gurfanar da shi a gaban kotu

Jigawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani mutum mai shekaru 46 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) na rundunar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Dutse ranar Talata.

Jihar Jigawa: An kama mai garkuwa da mutane
Jigawa: Jami'an tsaro sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shiisu ya ce wanda ake zargin da aka kama a ranar 28 ga watan Fabrairu, ana zargin dan tawagar da suka yi garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara 22, Hadiza Alhaji-Chadi kwanan nan a kauyen Marma.

Kara karanta wannan

Kano: Mutane 4 Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Bayan Ganduje Ya Rantsar Da Shugabannin APC

A cewar Shiisu:

“Ta hanyar bayanan sirri, rundunar ta samu nasarar cafke wani mai suna Ado Ahmadu mai shekaru 46 kuma mazaunin Marawaji a karamar hukumar Kirikasamma bisa laifin yin garkuwa da mutane."

Jami'in ya ce, a ranar 7 ga watan Janairu da misalin karfe 7 na safe, daya daga cikin mutanen kauyen Marma da ke karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Chadi, ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

Ya ce a wannan ranar da misalin karfe 3:30 na dare wasu ‘yan bindiga kimanin shida da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki gidan sa inda suka yi awon gaba da matarsa Hadiza Alhaji-Chadi ‘yar shekara 22.

A cewarsa, bisa la’akari da rahoton da kuma wasu al’amura masu alaka da sace mutane a jihar ne ya sa Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Aliyu Sale, ya shirya wani samame karkashin jagorancin jami’an leken asiri mai suna “Operation Flush Out”.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Kasa ta rufta da mutum 5 a garin taya abokinsu hakar kasar ginin aurensa

Hakazalika, ya ce samamen yana karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan 'yan sandan ne DCP Bashir Ahmad, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shiisu ya kara da cewa an kubutar da wanda aka sace ba tare da jin rauni ba a daya daga cikin ayyukan bayan da ‘yan sanda suka kai samame maboyar wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Suletankarkar.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Matasa sun fusata, sun damke yan bindiga biyu sun kona su kurmus

A wani labarin, wasu da ake zargin yan bindiga ne masu garkuwa da mutane sun rasa rayukansu a hannun mutane, kuma suka kona gawarsu kurmus a kauyen Anpam, karamar hukumar Mangu, jigar Filato.

Daily Trust ta rahoto cewa wasu fusatattun matasa ne suka halaka mutanen da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai

Rahoto ya nuna cewa kusan gidaje 13 mallakin Fulani fusatattun matasan suka kone a yankim bayan kashe mutanen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.