Cin Hanci: Shugaban EFCC ya goyi bayan kalaman Obasanjo kan masu neman gaje Buhari a 2023

Cin Hanci: Shugaban EFCC ya goyi bayan kalaman Obasanjo kan masu neman gaje Buhari a 2023

  • Shugaban hukumar EFCC ya ce maganar Obasanjo gaskiya ce, amma hukumarsa ba ta da hurumi har sai alkali ya yanke hukunci
  • Obasanjo ya yi ikirarin cewa da EFCC na aikinta yadda ya kamata da duk masu son gaje Buhari na ɗaure a gidan Yari
  • Bawa ya ce hukumar sa ta samu nasarori tun bayan zuwansa Ofis, wanda ba'a taɓa samu ba a tarihi

Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya bayyana goyon bayansa ga kalaman tsohon shugaban ƙasa, Chief Olusegun Obasanjo.

Daily Trust ta rahoto Cewa Obasanjo ya yi ikirarin cewa duk waɗan nan yan siyasan dake son ɗare wa kujerar Buhari a 2023, suna da tabon da ya kamata ace suna ɗaure a kurkuku.

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa
Cin Hanci: Shugaban EFCC ya goyi bayan kalaman Obasanjo kan masu neman gaje Buhari a 2023 Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Bawa, wanda ya yi hira da yan Jarida a Legas, ya ce hukumarsa ba ta da ikon hana yan siyasa neman takara duk da suna gaban Kotu, tun da akwai yuwuwar ba su da laifi har sai an tabbatar da sun aikata.

Kara karanta wannan

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

A kalamansa, Bawa ya ce:

"Baba ya yi gaskiya saboda wasu daga cikin su muna tafka shari'a a kansu, amma zata iya yuwuwa ba su da laifi har sai an tabbatar sun aikata laifin."
"Ko da mun kai lamarin gaban Kotu, matukar Alkali bai ayyana sun aikata laifin ba, suna da damar shiga takarar zaɓe, wannan shi ne gaskiyar halin da muka tsinci kan mu."
"Wasu lokutan yan jarida na ɗakko labaran wasun su da muka gurfanar a gaban Kotu, su yi rubutu a kan su dangane da yadda suka tattara bayanan su."

Shin wane canji Bawa ya kawo a EFCC?

Bawa ya ƙara da cewa sauyin da ya kawo a hukumar EFCC tun bayan kama aiki a matsayin shugaba shekarar da ta gabata ya haifar da sakamako masu kyau.

Kara karanta wannan

Wata Mata ta halaka dan uwanta tsoho dan shekara 75 daga fara faɗa, ta yi kokarin boye laifinta

A cewarsa, tun bayan kama aikinsa hukumar EFCC ta samu nasarar tabbatar da laifuka 2,220 a dukkan rassan ta dake faɗin ƙasar nan.

Bugu da kari, yace wannan shi ne adadi mafi yawa na kama mutane da aikata laifi da hukumar ta yi tun farkon kafa ta a tarihi.

Shugaban ya ƙara da cewa hukumar ta kwato Naira Biliyan N152.09bn da kuma dala miliyan $386.22m a Case daban-daban, inda ya ɗora da cewa EFCC ta kwato makudan kuɗaɗen ƙasashen duniya.

A wani labarin kuma Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

Jarumin Kannywood , Lawan Ahmad, ya tabbatar da shiga tseren takarar mamba mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin Katsina.

Jarumin wanda tauraruwarsa ke haskawa a shirin Izzar So da sunan Umar Hashim, ya fito siyasar ne karkashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262