Masu garkuwa da mutane sun sace mata da miji, sun hada da jariri mai wata 5
- Miyagun masu garkuwa da mutane sun kutsa cikin wani gida a Abaji da ke Abuja inda suka sace mata da miji tare da jinjirinsu mai wata 5
- Wani mazaunin yankin ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya tabatar da cewa an sako matar da jinjirin kuma sun yi awon gaba da mijin
- Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan babban brinin tarayya ta musanta faruwar lamarin inda tace suna kokarin ganin bayan ta'addanci a birnin
FCT, Abuja - An yi garkuwa da wani mutum, Hezekiah Franscis da matarsa, Josephine Hazekiah, da jinjirin su mai watanni biyar, Hanniel Hezekiah daga gidansu a Abattoir new extension cikin Abaji dake Abuja.
Daily Trust ta gano yadda lamarin ya auku a daren Juma'a.
Sai dai an saki matar mutumin da 'dan bayan tafiyar wasu mitoci daga gidan nasu, amma har yanzu mijin na hannun wadanda suka yi garkuwan dasu.
Da farko dai, wasu mazauna yankin sun tsegunta wa Daily Trust game da aukuwar lamarin, amma Josephine Adeh, kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, ta musanta rahoton.
A lokacin da aka tuntubi, DSP Adeh, ta ce, "Babu batun aukuwar lamarin cikin FCT."
Ta ce, hukumar ba za tayi kasa a gwuiwa wajen ganin ta tumbuko duk wasu ayyukan ta'addanci a cikin babban birnin, inda ta kara da cewa, jami'an tsaron hukumar na sa ido sosai a kan dukkan iyakokin da ke sada Abuja da sauran jihohi.
Sai dai daga baya matar wanda lamarin ya auku da shi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bada labarin yadda 'yan bindigan suka auka cikin gidansu misalin karfe 11:00 na daren Juma'a.
Ta ce, 'yan fashi da makamin sun dira ta katanga don samun shiga gidan.
Kuma ta bayyana yadda wasu daga cikin su suka yi wa gidan zobe, yayin da wasu suka lalata tagogin gidan, ta inda suka shiga cikin daki.
"Da farko sun fara zuwa sasan farko, inda kanwata ke bacci, suka lalata kofar, amma cikin sa'a basu ganta a maboyar ta ba. A lokacin ne suka shiga cikin asalin gidan, inda suka yi awon gaba da ni da mijina," a cewarta.
Ta ce, a lokacin da suka tafi dasu, bayan tafiya na wasu mitoci daga gidan, masu garkuwa da mutanen sun ce ta koma tunda tana shayar da 'da.
An yi kokarin jin ta bakin Adeh game da ikirarin da matar tayi, amma hakan bai yuwu ba, saboda bata amsa waya balle bada amsar sakonnin da aka tura ma ta.
Daily Trust ta ruwaito yadda wasu hatsabibai duk da 'yan bindiga suke kutsawa babban birnin tarayyar daga jihohin dake makwabtaka da ita, irin su Neja, kogi, Nasarawa, Plateau da Kaduna.
An kuma: Yaran marigayi Gana sun halaka mai karbar haraji da wasu mutum 3 a Benue
A wani labari na daban, an sake samun labarin yadda 'yan bindiga da ake zargin magoya bayan marigayi Terwase Akwaza, wanda ake wa lakabi da Gana ne suka halaka wani mai amsar haraji da wasu mutane uku a kauyen Imande Kundi a gundumar Mbache na karamar hukumar Katsina-Ala dake jihar Biniwe.
Al'amarin ya auku ne bayan kwana hudu kacal da 'yan bindigan suka kai wa wani yankin dake makwabtaka kwatankwacin harin a cikin gunduma daya, wanda yayi sanadiyyar lashe rayukan sarkin kauyen da masu zaman makoki guda takwas.
Wata majiya a yankin ta bayyana wa Vanguard yadda 'yan bindiga suka auka yankin a ranar Laraba misalin karfe 3:00 na rana, inda suka budewa mutane wuta.
Asali: Legit.ng