Da duminsa: Saudi Arabia ta dage haramcin saukar jiragen saman Najeriya a kasar

Da duminsa: Saudi Arabia ta dage haramcin saukar jiragen saman Najeriya a kasar

  • Kasar Saudi Arabia ta sanar da dage dakatar da jiragen saman Najeriya daga shiga kasar sakamakon barkewar cutar korona nau'in Omicron
  • Kasar Saudi Arabia ta sanar da dage takunkumin ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafin Saudi Gazette na Twitter
  • Sanya takunkumin ga jiragen Najeriya ya saka 'yan Najeriya sun fara tunanin za su yi Umra da Hajji ko a'a

Masarautar Saudi Arabia ta dage haramcin da ta saka wa jiragen saman Najeriya daga sauka a kasar sakamakon bayyana nau'in korona na Omicron.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an saka takunkumain a ranar 8 ga watan Disamban 2021, lamarin da yasa aka tsayar da shirin aikin Hajji da Umra a Najeriya.

Da duminsa: Saudi Arabia ta dage haramcin saukar jiragen saman Najeriya a kasar
Da duminsa: Saudi Arabia ta dage haramcin saukar jiragen saman Najeriya a kasar
Asali: Original

An sanar da wannan dage takunkumin a ranar Asabar, inda masarautar ta cire da yawa daga cikin dokokin dakile yaduwar cutar korona, lamarin da yasa aka fara saka ran yin aikin Hajji a 2022.

Kara karanta wannan

Gwanda in zama dan gudun Hijra da in dawo Najeriya, Dan Najeriya dake Ukraine

Kamar yadda sanarwar ta bayyana a shafin Saudi Gazette na Twitter, masarautar ta sanar da dakatar da saukar jiragen sama daga kasashe 17 na duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasashen sun hada da South Africa, Namibia, Botswana, Zimbabwe, Lesotho, Eswatini, Mozambique, Malawi, Mauritius, Zambia, Madagascar, Mauritius, Zambia, Madagascar, Angola, Seychelles, Jamhuriyar Congo da sauransu.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Saudi Arabia ta tabbatar da dakatar da saukar jiragen saman Najeriyan a wata takardar da Saudi Arabia Arabi ta aike wa kamfanonin jiragen saman.

Bayan dakatarwan, kamfanin Azman Air, kamfanin jiragen sama tilo daya da ke shiga kasar Saudi Arabia ya dakatar da shirin Umrah, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel