Yanzu-Yanzu: Fadar shugaban kasa ta bayyana sabuwar ranar da Buhari zai tafi Landan ganin Likita
- Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa ranar Lahadi 6 ga watan Maris, 2022, shugaba Buhari zai tafi Landan duba lafiya
- Tun farko shugaban ya tsara zarcewa Landan bayan kammala taron da ya kai shi Kenya, amma sai aka gan shi ya dira Abuja ranar Jumu'a
- Babban mai taimaka wa shugaban ta yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce tafiyar na nan ba'a soke ba
Abuja - Tafiyar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zuwa Landan domin ganin likita ta na nan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mutane sun yi mamakin ganin shugaban ƙasan ya dawo gida Najeriya ranar Jumu'a, maimakon zarcewa Birnin Landan kamar yadda fadarsa ta sanar.
Amma da aka tuntubi babban mai taimaka wa shugaban ƙasa ta bangaren watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce Buhari ya dawo Najeriya ne bayan kammala aikin da ya je Nairobi da wuri.
Game da ko shugaban ya fasa zuwa Landan ne, Shehu ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A'a, bai soke tafiya Landan ba, shirin na na kamar yadda aka tsara. Ya kammala abin da ya kai shi Kenya shiyasa aka ga ya dawo gida. Tafiya Landan na nan ranar Lahadi."
Buhari ya halarci bikin cikar shirin majalisar dinkin duniya (UNEP) karo na 50 a Nairob, Kenya, da nufin wucewa Landan na tsawon mako biyo domin a duba lafiyarsa.
Hadimin Buhari, Femi Adesina, shi ne ya bayyana shirin tafiya Landan na farko, a wata sanarwa da ya fitar a farkon makon da muke ciki, kamar yadda Channels tv ta rahoto
Adesina ya ce:
"Daga kasar Kenya, Shugaban ƙasa Buhari zai wuce Landan ganin likita, wanda zai kwashe mako biyu."
Sai dai mutane sun shiga rudani ranar Jumu'a, lokacin da Bashur Ahmad, hadimin shugaban ƙasan, ya sanar da isowar Buhari Najeriya.
Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina
"Shugaba Buhari ya dawo Abuja bayan halartar taron cikar shirin UNEP shekara 50 da ya gudana a Nairobi, ƙasar Kenya."
- Bashir Ahmad
A wani labarin na daban kuma Matar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a Kotu kan kisan Hanifa Abubakar
Matar wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, Jamila Muhammad, ta ba da shaida a Kotu bayan ya ce ba shi ya kashe ta ba.
Jamila ta faɗi yadda ya kawo mata yarinyar da kuma karyar da ya mata game da ita, har zuwa ranar da ya ɗauke ta da daddare bayan kwana 5.
Asali: Legit.ng