Da Dumi-Dumi: Kotu ta ba da umarnin a saki Matar Abdulmalik Tanko da ya kashe Hanifa

Da Dumi-Dumi: Kotu ta ba da umarnin a saki Matar Abdulmalik Tanko da ya kashe Hanifa

  • Kotun Majistire a Kano ta ba da umarnin a saki matar Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe Hanifa Abubakar
  • A ranar Alhamis, matar Jamila Sani, ta shaida wa babbar Kotun Kano gaskiyar abin da ta sani tun daga farko
  • Bisa haka Lauyan jiha ya nemi Kotun ta duba shaidar da ta bayan kan mijinta, ta ba da umarnin a barta ta tafi

Kano - Kotun Majistire dake Kano ta ba da umarnin sakin Jamila Sani, Matar Abdulmalik Tanko, wanda ya amsa kashe Hanifa Abubakar a Kano.

Daily Trust ta rahoto cewa Matar, wacce ake zargi da haɗa baki da maigidanta wajen sace Hanifa da kashe ta, ta samu yanci ranar Jumu'a.

Jamila ta bayyana gaskiyar lamari, lokacin da ta ba da shaida kan mijinta a babbar Kotun jihar Kano, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Dirama a Kotu: Saurayin da ake zargi da kashe budurwarsa ya koma mawaƙi da ya ga shaidu

Shari'ar kisan Hanifa
Da Dumi-Dumi: Kotu ta ba da umarnin a saki Matar Abdulmalik Tanko da ya kashe Hanifa Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Tun da farko dai lauyan jiha, Barista Lamido Soron Dinki, ya roki Kotu ta duba shaidar da matar ba bayar kan mijinta.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda Matar Tanko, Jamila Muhammad Sani, ta yi bayani dalla-dalla a gaban Kotu kan abinda ta sani game da kisan Hanifa.

Matar ta shaida wa Alkali duk abin da ya faru tun daga ranar da Tanko ya zo da yarinyar ƙarama gidanta, har zuwa ranar da ya ɗauke ta da daddare.

Abin da Jamila ta faɗa wa Kotu

Wani sashin bayaninta, Matar Tanko ta ce:

"Ya kawo yarinyar gidana, ya faɗa mun mahaifiyarta malama ce a makarantarsa, ta samu aiki a Saudiyya dan haka zata je Abuja ta sanya hannu a wasu takardun tafiya."
"Ta kara kwana biyu, sai ce mun ya yi ta kira shi wai kuɗi sun kare mata a Kaduna. Daga nan na daina tambayarsa saboda ya ce ba ta da kuɗin dawowa."

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa na fara daukan bindiga, Bello Turji a zantawarsa da yan jarida

"Bayan kwana 5 yace zai kaita gida, lokacin da daddare ne, na ɗauki kayan makarantarta na bashi, kawayenta na bacci lokacin. Na nemi ya bari sai da safe saboda suna bacci amma ya matsa."

Legit.ng Hausa ta zanta da wani lauya mai zaman kansa, Barista Tukur Badamasi, kan wannan lamarin na sakin matar Tanko, ya ce:

"A gani na Kotun majistire ta yi kokari ta yi abin da ya dace, duba da shaidar da ta bayar a babbar Kotu kuma kan mijinta na aure."
"Idan ka duba shari'ar baki ɗaya ita ba ta cikin sahun farko na mutanen da ake zargi, abin da ke kanta shi ne haɗa baki da ita, kuma ta yi wa Kotu bayanin komai, dan haka dai-dai ne a sake ta."

A wani labarin kuma Shaidu sun gabatar da abubuwa 10 da suka gano game da kisan Hanifa Abubakar

A zaman cigaba da sauraron ƙara kan kisan Hanifa Abubakar, gwamnatin Kano ta fara gabatar da shaidu.

Kara karanta wannan

Kamar almara: An haramtawa Magen Rasha shiga kasar wasanni bisa mamayar Ukraine

A ranar Laraba, Shaidu uku da aka gabatar sun mika wa Kotu abubuwa 10 da suka kwato a hannun waɗan da ake zargi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel