Karin bayani: Yau dinnan za a yi zama na biyu don sulhunta tsakanin Ukraine da Rasha
- A yau ne za a yi zama na biyu na tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha, wanda za a yi a Belarus
- A baya an zauna zaman sulhun, amma ba a cimma wata matsaya ta zaman lafiya, rahoto ya ce yau Alhamis za a sake zama
- Hukumomi daga Ukraine suun bayyana cewa, tuni wakilan kasashen biyu sun shirya haduwar a iyakar Belarus
Belarus - A yau ne wakilai daga kasashen Rasha da Ukraine za su gana a zagaye na biyu na tattaunawar sulhu a iyakar kasar Belarus.
Tashar talabijin ta CNN ta ba da rahoton cewa, Mykhailo Podolyak, mashawarci ga shugaban kasar Ukraine ya bayyana cewa wakilansu na kan hanyarsu ta zuwa tattaunawar.
Andrew Simmons na Aljazeera, dake dauko rahoto daga birnin Lviv da ke yammacin kasar Ukraine, ya ce babu wani sa rai da a zagaye na biyu na tattaunawar da za a yi na cimma wata yarjejeniya kan kawo karshen yakin.
Ya bayyana haka ne duba da zaman da aka yi a baya, inda yace ta yiwu an samu bambancin ra'ayoyi tsakanin wakilan kasashen biyu.
A cewar Simmons:
"Idan wani abu ya ta'azzara tun lokacin da suka tattauna a baya ranar Litinin, [kuma] a wancan lokacin sun roki bambanta batutuwan, babu wata manufa guda ta zaman."
Wannan tattaunawa dai na zuwa ne bayan da aka kammala zaman farko, inda aka tado da batutuwa da dama, amma ba a bayyana mafita ga dakatar da yakin ba.
Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa a baya ta tattaro muku rahotanni kan yadda kasar Rasha ta dumfari kasar Ukraine, lamarin da ya kai ga mutuwar fararen hula da dama a kasar.
Majalisar dinkin duniya ta fitar da rahoto, ta ce akalla mutane miliyan daya ne suka yi gudun hijira daga kasar ta Ukraine zuwa kasashen da ke makwabtaka dasu.
Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine
A bangare guda, kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya ne, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, suka nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.
Matasan da suka yiwa ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja babban birnin Najeriya kawanya, sun kuma sanya sunayensu a cikin wata rajista da ofishin jakadancin ya bayar.
Jaridar Guardian ta rawaito cewa jami'an ofishin jakadancin sun dakile yunkurin daukar hotunan mutane a bakin ofishin.
Asali: Legit.ng