Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince a mikawa Amurka Abba Kyari
- Daga karshe, gwamnatin tarayya ta yanke shawara kan mikawa kasar Amurka Abba Kyari
- Antoni Janar na tarayya yace ya gamsu da cewa babu siyasa cikin bukatar da Amurka ke yiwa Abba Kyari
- Kyari, yanzu haka yana tsare hannun hukumar NDLEA kan zargin harkallar hodar Iblis
Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta amince da bukatar Amurka, na a mika mata dakataccen DCP na yan sanda, Abba Kyari, bisa alakarsa da shahrarren dan damfara Abass Ramon aka Hushpuppi da wasu mutum hudu.
Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana hakan a karar da ya shigar gaban shugaban Alkalan babban kotun tarayya dake Abuja kan lamarin, rahoton Vanguard.
An shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022 karkashin dokar Extradition Act.
Wannan kara da ya shigar ya biyo bayan bukatar Abba Kyari da wakilin jakadan Amurka yayi a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Antoni Janar ya bayyana cewa lallai ya gamsu da cewa zargin da ake yiwa Abba Kyari ba tada alaka da siyasa kuma babban laifi ne.
Yace:
"Idan aka mikashi ga Amurka, ba za'ayi masa rashin adalci ba, ba za'a azabtar da shi ba, ba za'a hanashi yancinsa ba saboda launin fatar jikinsa, asalinsa ko siyasarsa ba."
Ya kara da cewa dubi ga laifukan da ake zarginsa da su, ba za'a ce an yi masa rashin adalci ba idan aka mika shi.
Hukumar aikin yan sanda PSC ta ce a sake sabon bincike kan Abba Kyari
Hukumar aikin yan sanda (PSC) ta umurci Sifeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali, ya kaddamar da sabon bincike kan alakar dake tsakanin dakataccen jami'i Abba Kyari, da dan damfara, Abbas Ramon, wanda aka fi sani da Hushpuppi.
A cewar Sahara Reporters, wannan umurni ya biyo bayan shawarar da Antoni Janar na kasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya bada.
Rahoton yace a ranar Laraba, 26 ga Junairu, Antoni Janar yace hujjojin dake cikin takardan binciken da aka gudanar basu da karfin da za'a kama Abba Kyari da laifi a kotu.
Abba kyari ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa
An samu bayanai akan yadda Kyari ya amsa tambayoyi akan zarginsa da damfarar dala miliyan 1.1 da wani fitaccen dan Instagram, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.
FBI ta zargi yadda Hushpuppi ya hada kai da Kyari wurin kama wani abokin harkarsa, Chibuzo Vincent, don barazanar fallasa damfarar dala miliyan 1.1 da ya yi ga wani dan kasuwar Qatar.
FBI ta Amurka ta ce Hushpuppi ya tura dala 20,600 cikin asusun bankin Kyari.
Sakamakon haka ne PSC ta dakatar da Kyari sannan ta samar da kwamiti na musamman don bincike (SIP) akan gano ko Kyari ya na da hannu a damfarar.
Asali: Legit.ng