Zamu hadu da Mai Martaba Sarkin Kano, Mai Kamfanin Air Peace, Allen Onyeama

Zamu hadu da Mai Martaba Sarkin Kano, Mai Kamfanin Air Peace, Allen Onyeama

  • Daga karshe, kamfanin Air Peace yayi magana kan haduwa da mai martaba Sarkin Kano
  • Mamallakin kamfanin ya bayyana cewa ba zai bari wannan sabani ya haifar da wani rikici
  • A cewarsa, tun Sarkin Kano na matashi yake zuwa ganin mahaifinsa marigayi Sarkin Kano Ado Bayero

Shugaban kamfanin jirgin Mr Allen Onyema ya bayyana cewa hukumomin kamfanin zasu ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, nan ba da dadewa ba don tattaunawa kan abinda ya faru.

Zaku tuna cewa tuna karshen makon da ya gabata ake musayar kalamai tsakanin fadar Sarkin Kano da Air Peace.

Onyeama ya bayyana cewa ba zai bari wannan rashin fahimta ya tada kura ba saboda Sarkin Kano mutum ne mai son zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Ko hannun Tinubu na rawa haka zamu zabeshi shugaban kasa a 2023, Jibrin

Allen Onyeama
Zamu hadu da Mai Martaba Sarkin Kano, Mai Kamfanin Air Peace, Allen Onyeama
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabannin kamfanin jaridar Daily Independent.

Yace:

"Ban san wannan abun ya tada tarzoma. Ban san Air Peace ya zama musababbin rikici a kasa."
"Na kasance mutum mai son zaman lafiya...tun lokacin da nike da kananan shekaru."
"Saboda haka ba zan bari ayi amfani da ni wajen raba kasar nan ba. Na dade da sanin Sarkin Kano tun yana Ciroma, lokacin da mahaifinsa ke da rai."
"Zamu hadu wata rana. Ba mutum ne mai son rigima ba kuma ina da tabbacin zai so ya hadu da ni kuma nima ina son haduwa da shi."

A cewar Onyema, babu wata matsalar da wannan sabanin zata haifar.

Masarautar Kano ta baiwa kamfanin Air Peace kwanaki 3 ta baiwa Sarkin Kano Hakuri

Kara karanta wannan

Air Peace vs Sarkin Kano: Muna baiwa kwastmominmu hakuri amma ba laifinmu bane

Shugaban tsare-tsare na masarautar Kano, Isah Bayero, ya baiwa Air Peace sa'o'i 72 su baiwa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, hakuri bisa wulakantashi da suka yi da jinkirta tafiyarsa.

Malam Isah Bayero ya bayyana hakan ranar Asabar yayin hira da wasu manema labarai a jihar Kano.

Yace wajibi ne kamfanin Air Peace ya amsa cewa yayi laifi wajen kin bin tsari, wanda haka ya sabbaba jinkirin Sarkin Kano a tashar jirgin Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel