Da dumi-dumi: Gobara ta sake kaca-kaca da sansanin yan gudun hijira a Borno

Da dumi-dumi: Gobara ta sake kaca-kaca da sansanin yan gudun hijira a Borno

  • Wani sansanin yan gudun hijira da ke karamar hukumar Mafa ta jihar Borno ya kone kurmus a ranar Laraba
  • An tattaro cewa gobarar ta kona gidajen yan gudun hijira na wucin gadi fiye da guda 100
  • Hakazalika, annobar wacce ba a san me ya haddasa ta ba ta kona kayan abinci da sauran muhimman abubuwa

Borno - Daily Trust ta rahoto cewa gobara ta sake tashi a sansanin yan gudun hijira da ke karamar hukumar Mafa ta jihar Borno a ranar Laraba 2 ga watan Maris.

Majiyoyi sun bayyana cewar mummunan lamarin ya sa daruruwan mutane sun zama marasa galihu sakamakon rasa muhallinsu da suka yi.

Hakan na zuwa ne yan makonni bayan irin haka ya afku a sansanin yan gudun hijira na Muna Al-Barnawai da ke Maiduguri.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Da dumi-dumi: Gobara ta sake kaca-kaca da sansanin yan gudun hijira a Borno
Da dumi-dumi: Gobara ta sake kaca-kaca da sansanin yan gudun hijira a Borno Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Lamarin wanda ya afku kimanin makonni biyu da suka gabata ya yi sanadiyar lalacewar gidaje sama da 3,000.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 12:00 na rana sannan ta kona wasu gidajen yan gudun hijira na wucin-gadi wanda ba a san adadinsu ba.

Wata majiyar agaji ta bayyana cewa gobarar ta kona kayayyakin abinci da wasu muhimman kayayyaki.

“Ba mu riga mun san abun da ya haddasa gobarar ba amma fiye da gidajen wucin gadi 100 sun kone. Muna aiki a kai yanzu.”

An tattaro cewa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Borno sun kashe wutan bayan kimanin awa daya.

Gobarar sansanin 'yan gudun hijira: Zulum ya kai ziyara, ya nemi a lissafa gidajen da suka lalace

A gefe guda, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA) da ta lissafa tare da mika bayanai kan adadin gidajen da gobara ya shafa domin gwamnatin jihar ta bayar da agaji yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Zulum ya bayar da umurnin ne a ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, yayin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da gobara ta cika da su a sansanin yan gudun hijira na Muna Elbadawy, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayar da sanarwa.

Gobarar wacce ta tashi a sansanin yan gudun hijirar da ke wajen Maiduguri, ya halaka rai daya sannan ya jikkata mutane 17 yayin da ya halaka matsuguni sama da guda 100. Sansanin na dauke da gidaje fiye da 10,000 da mutane 50,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng