‘Yan bindiga sun bindige basaraken gargajiya a jihar Ekiti
- Yan bindiga sun farmaki wani basaraken kasar Yarbawa, Oba Abdulmumini Orishagbemi na masarautar Aiyede da ke jihar Ekiti
- Maharan sun budewa motar basaraken wuta inda harbi ya same shi a kafar hagu
- An gaggauta daukarsa zuwa wani asibitin kwararru inda yake samun sauki
Ekiti - Wasu tsagerun yan bindiga sun harbi basaraken masarautar Aiyede da ke jihar Ekiti, Abdulmumini Orishagbemi.
Basaraken na a hanyarsa ta dawowa daga Ijero Ekiti lokacin da yan bindigar suka far masa a tsakanin Isan da Iludun, a karamar hukumar Ilejemeje da ke jihar, a daren ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, The Cable ta rahoto.
A cewar wata sanarwa daga kakakin sarkin, Bashir Adefaka, ya ce harbin da maharan suka yi, ya samu basaraken a kafa.
Adefaka ya ce an kwashi basaraken zuwa wani asibitin kwararru a Oye Ekiti domin samun kulawa kuma cewa yana samun sauki sosai.
Sanarwar ta zo kamar haka:
“Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farma Attah kuma basaraken masarautar Aiyede, jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, Mai martaba Oba Alhaji Abdul Mumini Adebayo Orishagbemi, a daren ranar Lahadi da misalin 9:30 na dare.
“Kabiyesi, wanda hukumar tsaro ta NSCDC ta janye masu tsaronsa kwanaki ba tare da bayar da dalili ba, na a hanyarsa ta dawowa daga Ijero Ekiti lokacin da miyagun suka far masa, a wani waje tsakanin Isan da Ilusun, a karamar hukumar Ilejemeje ta jihar.
“Yan bindigar sun bude wuta a motar SUV inda harsashi ya shiga kafar Kabiyesi na hagu. An gaggauta kai shi wani asibitin kwararru da ke Oye, karamar hukumar Oye Ekiti kuma yana samun sauki.
“Labari mai dadi, baya ga rayuwarsa da aka ceto, babu wanda ya raunata a cikin ayarinsa.”
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun sace amarya tare da hallaka mutum 8 a Neja
A wani labarin, yan bindiga da yawansu ya kai 100 sun farmaki wasu garuruwa a karamar hukumar Lavun da ke jihar Neja.
An tattaro cewar yan bindigar sun kai hari wajen wani taro na aure sannan suka sace amarya.
Sun kuma kashe mutane takwas sannan suka jikkata wasu da dama. Garuruwan da aka kai hari sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu, rahoton Arise tv.
Asali: Legit.ng