Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa

Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa

  • 'Yan ta'adda sun kutsa kauyukan kananan hukumomin Mashegu, Lavun da Wushishi na jihar Niger inda suka halaka rayuka 17 a sabon farmaki
  • Sun sheke dagacin kauye yayin da suka halaka Umar Ubegi, shugaban ma'aikatan Mashegu tare da mahaifinsa
  • Mazauna yankin sun ce miyagun sun fara barna tun daga ranar Juma'a har zuwa Asabar karfe takwas na dare inda suka shiga sama da kauyuka goma

Niger - A kalla rayuka 17 da suka hada da uba da dansa wasu miyagun 'yan ta'adda suka halaka a kauyukan kananan hukumomin Mashegu, Lavun da Wushishi dake jihar Niger.

Jama'a da yawa sun dinga barin gidajensu sakamakon farmakin wanda ya auku daga karfe 12 na rana zuwa karfe takwas na ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa
Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A karamar hukumar Mashegu, kauyukan da aka kai hari sun hada da Sabon-Rami, Igbede, Chekaku, Ubegi, Maishankafi da Poshi.

Babban sakataren yada labarai na shugaban karamar hukumar Mashegu, Mohammed A. Isah, ya sanar da manema labarai cewa shugaban ma'aikatan gwamnatin karamar hukumar, Umar Ubegi da mahaifinsa duk sun rasa rayukansu yayin farmakin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Miyagun 'yan ta'addan sun halaka dagacin kauyen Poshi da wasu mutum bakwai a Sahon-Rami da ke Maishankafi.

"Sun dinga shiga kauyuka a kan babura suna kashe jama'a tare da yin garkuwa da wasu. Sun sace shanun jama'a. A kalla yankuna 13 suka yi wa kaca-kaca kuma jama'a sun dinga barin gida.
"A halin yanzu duk hankula tashe suke a karamar hukumar mu. Wadannan mutanen tun Juma'a suke cin karensu babu babbaka. Kauyen Sahon-Rami ne suka kai fara kaiwa farmaki a ranar Juma'a. Duk sauran sai Asabar suka shiga," yace.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun dumfaro kauyuka a Filato, hakimai na ta kansu

A karamar hukumar Lavun kuwa, an kai wa kauyuka goma farmaki inda suka halaka mutum uku taare da sace wasu ukun.

Kauyukan da miyagun suka kai wa farmaki a karamar hukumar Lavun sun hada da: Egbako, Dabban, Kupa, Ndaruka, Tsogi, Mawogi, Yemi, Managi, Kanko da Gogaga.

Wani mazaunin Egbako, Yakubu Mohammed, ya ce:

"Sun fara luguden wuta tun karfe 12 na rana inda suka dinga shiga kauyuka daban-daban. A halin yanzu, mun samu gawawwaki uku, sun kuma sace wasu mutum uku."

Yankunan da wannan farmakin ya faru da su suna da nisan kilomita talatin da shida ne kacal daga Bida kuma kasa da nisan kilomita talatin daga fadar Etsu Nupe.

Daily Trust ta tattaro cewa, wannan farmakin ya datse kasuwar sati ta Batati da ke ci a titin Mokwa zuwa Bida yayin da 'yan kasuwa suka bar kayayyakinsu tare da gudun ceton rai.

'Yan ta'adda sun toshe titin Yawuri zuwa Koko, sun sheke rai 3 a farmakin

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa masu saka kuri'a wuta, sun halaka 5

A wani labari na daban, a ranar Asabar, 'yan bindiga sun tare titin birnin Yauri zuwa karamar hukumar Koko dake jihar Kebbi.

Ganau daga birnin Yauri mai suna Umar Bachelor, ya shaida wa Vanguard ta waya yadda 'yan bindiga daga Rijau cikin jihar Neja suka tare titin birnin Yauri zuwa Koko, inda suka halaka a kalla mutane uku da ke taso daga jihar Neja zuwa Sakkwoto, a cewar sa 'yan bindigan sun sheke direba da mutane biyu.

Ya bayyana yadda lamarin ya dauki tsawon awa daya, ba tare da dakatarwa ba, Vanguard ta ruwaito.

"Sun tare titin, sannan suka ci karen su ba babbaka na tsawon awa daya, inda suka tafi da kansu ba tare da tuhuma ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng