Matar Aure Mai Ciki Tayi Garkuwa Da Kanta, Ta Siya Gida Da Kudin Fansar Da Ta Karba Daga Masoyinta Na Facebook
- Kotu ta bada umurnin a tsare wata matar aure mai juna biyu, Jamila Ardo kan zarginta da garkuwa da kanta a Adamawa
- Karar da aka shigar a kotun ya ce Jamila ta hada baki da wani Abdulaziz ne wurin karyar garkuwar kuma suka karbi N2m daga masoyinta na Facebook
- Daga bisani bayan masoyin ya biya kudin fansar ta kira shi ta ce an sake ta amma bai gamsu ba hakan yasa ya yi korafi daga bisani bincike ya yi halinsa
Adamawa - An tsare wata matar aure, Jamila Ardo, bisa zargin ta da yin garkuwa da kanta tare da karbar kudin fansa daga hannun masoyinta, rahoton The Punch.
Ardo, yar asalin garin Wuaru Jabbe a karamar hukumar Yola South na Jihar Adamawa, ta yi garkuwa da kanta sannan ta karbi N2m daga Mallam Adamu Ahmed mazaunin Abuja.
Matar, mai shekaru 25, wanda aka ce an hada baki da wani Abdulaziz don yin garkuwa da kanta saboda ta yaudari masoyinta, ta yi nasara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ce ta yi amfani da kudin da ta samu ta siya gida.
Wacce ake zargin sun fara soyaya ne da Ahmed bayan sun hadu a Facebook, amma mutumin bai san cewa ita matar aure bane.
Punch Metro ta rahoto cewa duk soyayyan a yanar gizo suke yi, ba su taba haduwa ba.
Bayanin yadda abin ya faru ya nuna Abdulaziz ya hada baki da Ardo, ya kira masoyinta, ya sanar da shi an yi garkuwa da ita ya bukaci ya biya kudin fansa.
Yayin tattaunawa don a sake ta, Adamu ya ji Ardo tana kuka, tana rokon ya biya kudin fansar.
Adamu ya biya kudin cikin wani asusun banki mai suna Amina Mohammed a cewar rahotanni.
"Bayan aike wa da kudin, masoyiyar ta Adamu ta sanar da shi cewa masu garkuwan sun sake ta.
"Daga nan ya fara shakku ya shigar da korafi a hukumar bincike a ranar 16 ga watan Nuwamban 2021," a cewar karar da aka shigar.
Daga bisani yan sanda sun kama wanda ke da asusun bankin da aka tura kudin, wani Mohammed.
Punch Metro ya gano cewa wanda ake zargin ta amsa cewa kawarta, Ardo ce ta bukaci ta bata lambar asusun bankinta domin wani abokinta zai tura mata kudi.
Kafin abin ya fito fili, mijin Ardo shima ya tambayi inda ta samu kudi sai ta yi ikirarin cewa yan uwanta suka tura mata.
An gurfanar da Ardo a kotu
Daga bisani an gurfanar da ita a gaban kotun Majistare ta I a Yola kan zargin hadin baki da nufin aikata laifi da garkuwa wanda sun saba wa sashi na 60 da 248 na Penal Code.
Ta musanta zargin da ake mata.
Dan sanda mai gabatar da kara, Insp. Abubakar Nurudeen ya roki kotu ta bashi damar neman shawara daga ofishin harkokin shari'a na jihar.
Lauya wanda aka yi kara ya roki a bawa Ardo damar ganin likita saboda halin da ta ke ciki kuma a basu lokaci su shirya kare ta.
Alkalin kotun, Digil, ya amince da hakan ya kuma daga cigaba da shari'ar zuwa ranar 10 ga watan Maris na 2022 ya kuma umurci a tsare wanda aka yi karar.
Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki
A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.
Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.
Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.
Asali: Legit.ng