Buhari: Ba Zan Zarce 2023 Ba, Na Yi Rantsuwa Da Kur'ani
- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jadada cewa ba zai wuce wa'adi biyu da kundin tsarin mulki ta tanada masa ba
- Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a, ranar Alhamis a fadar Sarkin Lafia, Jihar Nasarawa yayin da ya kai ziyarar aiki a jihar
- Buhari ya kuma gargadi shugabanni da masu rike da mukaman siyasa su rika takatsantsan da amanar da suka dauka musamman duba da cewa sun rantse da Kur'ani
Jihar Nasarawa - Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis a Lafia, Jihar Nasarawa, ya ce ya yi rantsuwa da Kur'ani mai tsarki cewa wa'adi biyu kawai zai yi a ofis, rahoton The Punch.
Ya ce ya kamata shugabanni da ke yin rantsuwar kama aiki da littafai masu tsarki su yi takatsantsan da jagorancin da Allah da al'umma suka basu.
Buhari, wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a Nasarawa, ya yi wannan furucin ne a fadar Sarkin Lafia, Sidi Muhammad I, inda ya jadada cewa ba zai wuce wa'adi biyu da kundin tsarin mulki ta kayyade ba.
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen watsa labari, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ambaci Buhari na cewa sarautar gargajiya ba shi da wa'adi amma zababun shugabanni na demokradiyya suna da wa'adi.
Shugaban kasar ya ce:
"Ba zan iya wuce wa'adi biyu a ofis ba, kuma na yi rantsuwa da Kur'ani da cewa zan girmama kundin tsarin mulkin Najeriya.
"Idan an aje siyasa a gefe, duk lokacin da aka saka mutum ya rantse da Kur'ani, ya kamata su yi takatsantsan. Ya zama dole mu rike amanar da Allah ya bamu. Na ga tsaffin gwamnoni a nan, ina fatan zan zama tsohon shugaban kasa."
Asali: Legit.ng