El-Rufai ya fallasa alakar da gwamnati ta gano tsakanin 'yan sanda, sojoji da 'yan bindigan Najeriya
- Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce gwamnati ta binciko alaka tsakanin wasu jami'an 'yan sanda, sojoji da 'yan bindiga a kasar nan
- Gwamnan ya ce abun takaici ne yadda aka samu masu cin amanar kasa, amma har yanzu babu shaidu gamsassu kan wannan al'amari
- A cewar Malam Nasiru, gwamnati za ta dage matuka wurin dakile hanyar samun kudi ga 'yan ta'adda saboda irin barnar da suke tafkawa
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce rahotannin binciken farko sun bayyana wata alaka tsakanin 'yan sandan Najeriya da sojoji tare da 'yan bindiga da suka addabi al'umma.
Ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da tawagar yada labarai ta fadar shugaban kasa a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
A yayin martani kan zargin cewa ko an samu wasu 'yan ta'adda da suka ratsa ta cikin tsarin tsaron kasar nan, El-Rufai ya ce:
"Eh, mun damu kuma ba za a ce abu ne da ba zai yuwu ba. Na kan yi jinkiri wurin amsa wannan tambayar. Binciken farko a kan masu daukar anuyin Boko Haram ya nuna alaka tsakanin wasu 'yan bindiga da jami'an 'yan sanda da na sojojin Najeriya. Suna da alaka sosai da 'yan bindigan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Toh don haka akwai hatsari. A kowanne tsari, ana iya samun masu cin amanar kasa kuma mun damu da hakan. Amma har a yau, ba mu da shaidu gamsassu. Ina tunanin sai mun yi aiki tukuru a kan hakan
“Kamar yadda nace, akwai bukatar mu zakulo masu daukar nauyin ta'addanci da kuma hanyar da ake bi domin kudin da kayan aiki su kai ga 'yan ta'addan saboda suna son hargitsa kasar nan. Ina da tabbacin makuden kudi ne," yace.
El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga
Ya ce idan gwamnati za ta iya dakile hanyar samun kudin 'yan bindiga, ta kwace kudi tare da datse hanyar samu makamansu, kashi hamsin na yakin za a iya cewa ta yi galaba.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamnan ya ce ta'addanci a arewa maso yamma ya fi rikicin Boko Haram kamari idan aka duba yawan mutane da aka kashe da wadanda aka sace.
Ngige: Ba don kwarewar mulkin Buhari ba, da yanzu 'yan Najeriya suna neman mafaka a Nijar da Kamaru
A wani labari na daban, Chris Ngige, ministan kwadago, ya ce da a ce ba a samu jajirtaccen mulki irin na shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da yanzu 'yan Najeriya sun zama 'yan gudun hijira a Kamaru da Nijar.
TheCable ta ruwaito cewa, Ngige ya sanar da hakan ne a ranar Laraba bayan an bashi digirin girmamawa a INSLEC a Abuja.
Ministan ya kara da cewa, da babu gogewar mulki irin ta Buhari, da yanzu kasar nan ta kasance cikin rikici kamar Venezuela.
Ya kamata a ba mutanen Legas tikitin shiga Aljanna kyauta sabida wahalar cunkoso, inji Malam El-Rufa'i
Asali: Legit.ng