Wazirin Katsina ya yi murabus daga kan kujerarsa bayan wata takaddama da ta biyo jawabinsa a Ilorin
- Mai girma Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga, ya yi murabus daga kan kujerarsa
- Hakan ya biyo bayan takaddama da ya shiga tsakaninsa da majalisar masarautar kan tattauna batutuwan rashin tsaro a Ilorin, jihar Kwara, ba tare da yardar ta ba
- Bayan ya amsa tuhume-tuhume uku da majalisar ke yi masa, sai ya gabatarwa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardarsa ta ajiye sarautarsa
- A kwanan nan ne dai Lugga ya bayyana yadda rashin tsaro ya tilastawa wasu hakiman garuruwa takwas yin kaura zuwa Katsina da kuma rufe makarantu
Katsina - Farfesa Sani Abubakar Lugga, Wazirin Katsina, ya yi murabus daga majalisar masarautar jihar.
Hakan ya biyo bayan tuhumar da majalisar ta yi masa kan cewa ya tattauna batutuwan rashin tsaro a Ilorin, jihar Kwara, ba tare da yardar masarautar ba.
A ranar 14 ga watan Fabrairu ne Farfesa Lugga ya halarci wani taro a Ilorin inda ya bayyana cewa yawan hare-haren yan bindiga ya yi sanadiyar rufe makarantu a kananan hukumomi takwas na jihar Katsina.
Farfesa Lugga ya ce lamarin ya kai ga har hakiman kananan hukumomin takwas sun koma Katsina, babbar birnin jihar da zama sakamakon hare-haren.
Sai dai, hakan bai yiwa majalisar masarautar Katsina dadi ba, inda ta aike masa da tuhuma.
A takardar da yake martani ga tuhumar da aka masa, Farfesan ya amsa lamura uku da majalisar ke tuhumarsa a kai sannan daga bisani ya gabatarwa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardarsa ta ajiye sarautarsa., Daily Trust ta rahoto.
Haka kuma ya yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Katsina tare da neman gafararsa idan har hukuncin da ya dauka ya sosa masa rai, rahoton Katsina City News.
Yunkurin jin ta bakinsa ya ci tura amma wata majiya abun dogaro ta ce wani daddaden rikici da ke kasa ne ya yi sanadiyar murabus dinsa.
Majiyar ta ce:
“Eh da gaske ne cewa Mai martaba, Wazirin Katsina ya mika takardar murabus dinsa, amma ina so ku sani cewa lamuran da suka kai ga murabus din nasa bai da alaka da abubuwan da suka faru kwanan nan sakamakon maganganunsa a Ilorin.
“Waziri mutum ne mai karamci da zai fadawa masu madafun iko gaskiya, duk dacinta, kuma wannan ba shine karo na farko da yake irin wannan sharhi na bari duniya ta san gaskiyar halin da ake ciki ba, amma kun san yanzu ba kowa ne ke son jin gaskiya ba kuma Waziri zai iya sadaukar da komai don kare mutuncinsa.”
Majalisar masarautar ta tabbatar da murabus din nasa
Da yake magana a madadin majalisar masarautar, Kauran Katsina, Alh. Nuhu Abdulkadir Rimi, ya tabbatar da ci gaban, cewa an samu takardar murabus din nasa.
Ya kara da cewar majalisar za ta tattauna a kan sannan ta yanke hukunci kan lamarin.
El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni
A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ta’addanci a arewa maso yamma ya fi na rikicin Boko Haram muni duba ga yadda adadin mutanen da ake kashewa da sacewa yake hauhawa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, yayin tattaunawa da mako-mako da tawagar labarai na fadar shugaban kasa ta shirya a fadar Villa, Abuja, Daily Trust ta rahoto.
Ya bayyana bukatar samar da shiryayyen mafita da kuma mayar da hankali wajen kawo karshen miyagun da ke amfani da kayayyakin aiki da suka fi na rundunonin tsaronmu inganci.
Asali: Legit.ng