Harkallar kwaya: Kotu a Abuja ta ce NDLEA ta duba bukatar belin Abba Kyari cikin awa 48

Harkallar kwaya: Kotu a Abuja ta ce NDLEA ta duba bukatar belin Abba Kyari cikin awa 48

  • Kutun tarayya da ke Abuja ta nemi a gaggauta duba yiwuwar ba da belin Abba Kyari da ke tsare a hannun NDLEA
  • Abba Kyari ya shigar da kara ne, inda yake neman a ba da belinsa sannan a biya shi diyyar kama shi ba bisa ka'ida ba
  • Alkali daga nan ya dage kara, ya ce za a duba yiwuwar ba da belin Abba Kyari a ranar Litinin, 28 ga watan Fabrairu

FCT, Abuja - Wata babbar kotu a Abuja, a ranar Alhamis, ta umurci hukumar NDLEA, cikin sa’o’i 48, ta amsa bukatar da DCP, Abba Kyari, wanda a halin yanzu yake hannunta, ya shigar na neman belinsa bisa rashin lafiya.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da wannan umarni ne a ranar da hukumar NDLEA ta yi ikirarin cewa ba a kai mata bukatar Kyari ba, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Abba Kyari da NDLEA na ci gaba da samun sabani
Da dumi-dumi: Kotu a Abuja ta ce NDLEA ta duba bukatar belin Abba Kyari cikin awa 48 | vanguardngr.com
Asali: Twitter

Lauyan hukumar Mista Mike Kasa, ya shaida wa kotun cewa har yanzu bai samu kwafin bukatar belin da ke kunshe da karar Abba Kyari mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22 ba.

Sakamakon haka, cikin wani dan takaitaccen hukunci mai shari’a Ekwo, ya umurci bangarorin biyu da su koma su daidaita tsakaninsu, duk da cewa ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Litinin don sauraron bukatar neman belin Kyari.

Abba Kyari ya maka gwamnati a kotu, ya fadi bukatunsa

DCP Kyari, a cikin karar da ya shigar kan gwamnatin tarayya, ya kalubalanci ci gaba da tsare shi a hannun hukumar ta NDLEA.

Daga cikin abubuwan da ya roki kotu da ta umurci gwamnati akwai biyansa Naira miliyan 500 na diyya da kuma rubuta takardar neman gafara a cikin jaridun Najeriya guda biyu kan cin zarafin sa da aka yi ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare Abba Kyari da abokan harkallarsa 6

Takardar karan Kyari ta bayyana dalilai da bukatun da ya bijiro dasu gaban alkali na tauye hakkinsa, inda ya bayyana dalilai da ke nuna an tsare shi ba bisa ka'ida ba, kana an aje shi a hannu NDLEA na tsawon kwanaki ba a kai shi kotu ba.

A makasudin farko na bukatarsa, ya roki kotu da ta bayar da umarnin a sake shi da sunan beli domin samun damar kula da lafiyarsa.

Kyari, ya shaidawa kotu cewa yana fama da ciwon sukari; hawan jini da ciwon zuciya mai tsanani da ka iya haddasa mutuwa.

Bayan sauraran batutuwa da duba da nazari, daga nan ne Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu, don sauraron bukatar belin Abba Kyari, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Sharri aka min, ina da ciwon sukari da hawan jini: Abba Kyari ya kai karar gwamnati kotu

Kara karanta wannan

An tsare ni ba bisa ka’ida ba: Abba Kyari ya nemi diyyar N500m a hannun NDLEA

A wani labarin, DCP, Abba Kyari, wanda a halin yanzu yake hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, bisa zarginsa da hannu a safarar miyagun kwayoyi, a ranar Litinin, ya maka gwamnatin tarayya a kotu, Vanguard ta ruwaito.

Kyari, a cikin karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, yana rokon kotu da ta tilasta wa hukumar NDLEA ta bayar da belinsa bisa dalilan rashin lafiya, har zuwa lokacin da za a saurari kararsa tare da yanke hukuncin neman tabbatar laifinsa.

A cikin karar da ya shigar ta hannun lauyar sa, Mrs PO Ikenna, tsohon shugaban rundunar leken asiri ta IRT, ya shaida wa kotun cewa ana tsare da shi ne “saboda zargin karya da aka kakaba masa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.