Shugaban 'yan bindiga, Dullu Kachalla, ya sassauta kudin haraji ga mazauna saboda sun gagara biya
- Dullu Kachalla, shugaban yan bindigar da suka addabi al'ummar jihar Zamfara ya ragewa wasu garuruwan da suka kakabawa haraji kudin da za su biya
- Kungiyar dai ta daurawa garuruwan irnin-Yero, Jangeru, Tubali, Kware, da sauran kauyukan da ke makwabta na karamar hukumar Shinkafi biyan haraji don hana kai masu hare-hare
- Mazaunan dai sun hada naira miliyan biyar cikin tara da kungiyar ta nemi su biya, inda suka gabatar mata da shi a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu
Zamfara - Shugaban yan bindiga, Dullu Kachalla, ya yafewa mazauna wasu garuruwan da suka kakabawa haraji sauran kudaden da ake binsu bayan sun gaza biyan cikakken kudin a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, HumAngle ta rahoto.
Kachalla mai shekaru 33 da kungiyarsa sun daurawa wasu garuruwan jihar Zamfara bakwai biyan harajin naira miliyan 40 domin hana su kai masu hari.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke yawan fama da hare-haren yan bindiga a Najeriya kuma yan ta’addan kan yi musu barazana da biyan haraji don guje ma hare-harensu.
Bayan bukatar Kachalla, mazauna garuruwan Birnin-Yero, Jangeru, Tubali, Kware, da sauran kauyukan da ke makwabta na karamar hukumar Shinkafi a jihar sun hada wasu kudade amma ba su hada cikakken abun da ya bukata ba.
Jabir Alhazai, wani mazaunin Shinkafi, ya fada ma HumAngle cewa:
“Koda dai yan bindigar karkashin jagorancin Kachalla sun kakabawa kauyuka bakwai biyan naira miliyan 40 da farko, daga bisani sun yarda a zabtare kudin zuwa naira miliyan 9 bayan tattaunawa da dattawan yankin.”
Ya kara da cewar mazauna yankin sun yi nasarar hada naira miliyan 5 daga cikin kudin wanda suka gabatar da shi ga kungiyar ta’addancin a ranar Laraba.
Ya kara da cewa:
“Mun ajiyewa yan bindigar zunzurutun kudin, inda muka nemi yafiyar sauran naira miliyan 4 da ya rage. Shugaban yan ta’addan ya fada mana cewa tunda talauci na damun mu na gaza cika kudin, mu biya Karin naira miliyan 1. Sai ya yafe mana sauran miliyan 3 don zaman lafiya.”
Birnin-Yero, Jangeru, Maniya, Tubali, Kware da sauran kauyukan da ke kewaye a karamar hukumar Shinkafi na zaune cikin tsoro da fargaba sakamakon yawan hare-haren yan bindiga.
Mansur Mamman, wani mazaunin Birnin Yero ya ce:
“Mun ta kai rahoto ga mahukunta da hukumomin tsaro domin kawo agajin gaggawa ga al’umma karkashin wadannan kungiyoyin yan ta’adda amma babu wani abun nunawa.
“Saboda wannan tsoro na hare-haren yan ta’addan da ke yawan kashe-kashen mutane, garkuwa da mutane da kuma fashin shanu ne yasa muka yanke shawarar hadawa yan ta’addan kudin don guje ma mai afkuwa.”
Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara
A gefe guda, mun ji a baya cewa mazauna garuruwa biyar da ke karkashin yankin Kurya Madaro a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu bayan yan bindiga sun koma yiwa matansu da yayansu mata fyade saboda rashin biyan kudin harajin da suka daura masu.
An tattaro cewa mazauna garuruwan da abun ya shafa sun zabi tserewa don tsira daga ci gaban hare-hare bayan sun gaza biyan yan bindiga naira miliyan 2 da suka daurawa kowannensu.
A wata hira da jaridar Tribune, wani mazaunin Balankadi, Malam Rabi'u Abubakar, wanda ke samun mafaka a wajen garin, ya ce yan bindigar sun ce lallai sai sun biya naira miliyan 2 kafin su barsu su samu zaman lafiya.
Asali: Legit.ng