Tashin hankali: 'Yan bindiga sun dumfaro kauyuka a Filato, hakimai na ta kansu
- Hare-haren yan bindiga ya tilastawa hakimai a yankin Bashar da ke karamar hukumar Wase ta jihar Filato barin gari ba shiri
- An tattaro cewa masu garkuwa da mutane na ta kaddamar da hare-hare tare da karbe ragamar iko a wasu garuruwa a yankin Wase
- Wani mazaunin yankin ya ce yan bindigar kan sace mutane tare da neman kudin fansa, sannan cewa su kan kashe wanda bai da kudin biya ko su daddaure shi
Plateau - Wani rahoton Daily Trust ya nuna cewa hakimai a yankin Bashar da ke karamar hukumar Wase ta jihar Filato sun gudu sun bar gari a yanzu haka, sakamakon hare-haren yan bindiga.
Garin Bashar ya kasance mahaifar mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Ahmed Wase.
Abdullahi Usman, wani mazaunin kauyen Sabon Gari, ya bayyana cewa hakiman kauye da saura mazauna sun tsere.
Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja
Ya ce:
“Masu garkuwa da mutanen sun kai hari sannan suka sace mazauna kauyukan sannan suka nemi a biya kudin fansa. Idan ba ka da kudi, saisu kashe ka. A wasu lokutan, saisu daure mutum da igiyoyi.
“A ranar Lahadi, sun farmaki kauyen Sabon Gari sannan suka kashe mutane uku. A jiya (Talata), sun kashe mutane biyu a kauyen Yalun. Muna cikin gagarumin matsala. A yanzu muna hannun masu garkuwa da mutane. Tuni hakiman garuruwan Bangalala, Kinashe, Aduwa da Achale suka tsere daga yankunansu. A yanzu kauyen na karkashin kulawar masu garkuwa da mutane.”
Abdulhamid Cikaaiki, wani mazaunin kauyen Bunyum, ya kuma fada ma Daily Trust cewa suna shirin barin kauyen domin masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyukan da ke kewaye da Bunyum kuma ana ta kai masu hari.
Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ba domin baya amsa waya.
Sai dai, kakakin Operation Safe Haven, Major Ishaku Takwa, yace dakarun soji sun amsa kira a safiyar ranar Talata game da hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane a Wase.
Ya ce:
“Sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa tare da ceto wanda abin ya shafa. Sojojin sun kuma kashe biyu daga cikin ‘yan fashin tare da kwato bindiga kirar AK-47 na masu garkuwa da mutane da harsashi 17.”
Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna
A wani labarin, yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in tsaro yayin da suka kai farmaki garin Rigachukun da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Lamarin ya afku ne a safiyar ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cewar wasu shaidu, an yi awon gaba da jami’in tsaron ne tare da wasu mazauna yankin.
Asali: Legit.ng