Yan bindigar da suka sace kansila a Sokoto sun nemi a biya kudin fansa miliyan N60
- Masu garkuwa da mutanen da suka sace kansila da wasu mutane takwas a kauyen Yar Tsakuwa da ke jihar Sokoto sun tuntubi yan uwansu
- Maharan sun nemi a tattara naira miliyan 60 domin fansar mutanen da suka sace a ranar Asabar da ta gabata
- Da yan uwan suka nemi ragi daga gare su, sai kawai yan bindigar suka kashe wayarsu
Sokoto - Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutane tara ciki harda wani kansila mai ci a kauyen Yar Tsakuwa da ke karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto, sun nemi a biya naira miliyan 60 kudin fansa.
Daily Trust ta rahoto cewa wani mazaunin yankin, Nazifi Abdullahi, ya bayyana cewa yan bindigar sun kira yan uwan wadanda aka sace sannan sun nemi su hada kudin.
Abdullahi ya ce:
“Sannan a lokacin da yan uwan wadanda aka sacen suka nemi ragi, sai suka kashe wayarsu. Ba mu san yadda za a iya hada wannan makudan kudi ba saboda na san daya daga cikin wadanda aka sace wanda da kyar yake daukar dawainiyar iyalinsa.
“A zahirin gaskiya, shi da iyalinsa suna zaune ne a gidan aro tun bayan da gidansu ya rushe wasu watanni baya.”
Mun kawo a baya cewa yan bindigar sun kai mamaya kauyen da misalin karfe 12:00 na tsakar daren ranar Asabar sannan suka ta kai farmaki har zuwa 2:30 na dare.
Hakazalika mun ji cewa diyar wani tsohon kansila da ke yankin, Alhaji Abdullahi Garba, na cikin wadanda aka sace.
Daily Trust ta rahoto cewa diyar tsohon kansilar sun zo kauyen ne domin halartan wani taron suna na jikansu, domin tun dama sun bar kauyen sakamakon hare-haren rashin imani da yan bindiga ke kaiwa.
Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun hallaka 8, sun sace da dama a Neja
A wani labarin, mun ji cewa, akalla mutane takwas ne aka kashe, yayin da aka sace 14 da suka hada da mata biyar a kauyukan Gpekure, Makuba da Galapai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Rahoto ya tattaro cewa, al’ummomin sun kasance cikin farmakin ‘yan ta’adda tun daren Juma’a da suka fara kai hari a Gpekure, inda suka kashe mutane bakwai tare da sace wasu bakwai.
Hare-haren sun tilastawa mazauna yankin da dama musamman mata da yara yin gudun hijira zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Zumba da Gwada da kuma makarantar Sakandare ta Gwamnati (GDSS) da ke Shiroro.
Asali: Legit.ng