Malaman frimare sun yi addu'o'i na musamman don rokon Allah yasa a biya su albashinsu a Neja

Malaman frimare sun yi addu'o'i na musamman don rokon Allah yasa a biya su albashinsu a Neja

  • Malaman makarantun firamare na Jihar Neja sun shirya taron addu’o’i na musamman don fatan Ubangiji ya kai musu dauki a biya su albashin su
  • Tun a ranar 10 ga watan Janairu malaman suka tafi yajin aiki yayin da makarantu suka koma zango na biyu duk don gwamnatin jihar ta motsa ta biya su hakkin su
  • Makwanni 7 kenan da kungiyar malamai ta kasa ta bukaci malaman su zauna gida, kawo yanzu, ba a ji komai ba daga gwamnatin jihar har ma’aikatar ilimi

Neja - Malaman makarantun firamaren gwamnati na Jihar Neja sun shirya taron addu’o’i na musamman da yakinin Ubangiji ya kai musu dauki gwamnati ta biya su albashin su, Daily Trust ta ruwaito.

Tun ranar 10 ga watan Janairu malaman suka fara yajin aiki bayan makarantu sun koma zango na biyu saboda gwamnatin ta ki kawo musu mafitar matsalolin su.

Kara karanta wannan

Shiga yajin-aikin ASUU ke da wuya, Malaman FCE sun soma barazanar rufe makarantu

Neja: Malaman firamare sun fara addu'o'i na musamman don Allah ya kawo musu dauki a biya su albashinsu
Malaman frimare a Neja sun yi addu'o'i na musamman don fatan Allah yasa a biya su albashinsu. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Bayan makwanni bakwai da kungiyar malamai ta kasa, NUT, ta umarci malaman makaranta da su zauna a gidajen su har sai gwamnati ta kawo karshen matsalar su, har yanzu gwamnatin jihar har ma’aikatar ilimi ba su yi komai akai ba.

Yanzu haka daliban sun kwashe watanni biyu cikin watanni uku na zangon karatun a gida.

Limamai da fastoci sun taru a hedkwatar NUT don yin addu’o’i

Daily Trust ta ruwaito yadda shugaban NUT na jihar, Akayago Adamu Mohammed; da mataimakin sa kuma sakatare janar, Labaran Garba, suka rubuta wata takarda wacce suka nuna damuwarsu akan yadda ake cutar da malaman makarantun firamaren inda suka ce hakan zai shafi rayuwar yaran da ba a koyar da kyau ba a makarantun gwamnati.

Kamar yadda takardar ta bayyana:

Kara karanta wannan

N-Power: Gwamnatin Tarayya za ta gwangwaje matasa 300, 000 da kudin jari inji Minista

“Ilimi kullum kara tabarbarewa yake yi yana kara shiga mawuyacin yanayi.”

Sun yi taron don yin addu’o’i a Hedkwatar kungiyar malaman da ke Minna inda limamai da fastoci suka taru suna karanta Qur’ani da Bibul.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164