Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari
- Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta dakatar da wasu jami'ai da ke tare da Abba Kyari a zargin harkallar kwayoyi
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da hukumar NDLEA ta sanar da neman Abba Kyari tare da kama shi da aka yi
- Abba Kyari da wasu mutum hudu 'yan tawagarsa na kan zargin safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa
FCT, Abuja - Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da ACP Sunday Ubua da ASP James Bawa daga aiki da mukamansu da ayyukan ofisoshinsu daga ranar Litinin 14 ga Fabrairu, 2022.
Jami’an ‘yan sandan biyu na aiki ne a karkashin DCP Abba Kyari da aka dakatar a cikin tawagar leken asiri ta IRT ta rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Wannan batu dai na kara fitowa ne yayin da ake ci gaba da binciken Abba Kyari da tawagarsa bisa zargin kulla harkallar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
A cewar mai magana da yawun PSC, Ikechukwu Ani:
“An kuma yi zargin cewa suna da hannu wajen kama hodar ibilis a halin yanzu tare da mika su ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa.”
Daga ina batun dakatar da jami'an ya fito
Hukuncin hukumar na kunshe ne a cikin wata wasika da ta aikewa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, mai kwanan wata 16 ga watan Fabrairu, 2022.
Wasikar an ce tana dauke da sa hannun mai shari’a Clara B. Ogunbiyi (mai ritaya) na kotun koli da kuma Alhaji Musiliu Smith, Sufeto Janar na 'yan sanda mai ritaya.
Hukumar ta bayyana cewa bisa tanadin dokar ma’aikatan gwamnati mai lamba 030406, ta amince da dakatar da jami’an har sai an kammala bincike kan zargin da ake yi musu.
Hukumar ta kuma umurci Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya kuma lura cewa DCP Abba Kyari, wanda kafin zargin NDLEA dama yana kan dakatarwa, zai ci gaba da kasancewa har sai an kammala bincike.
An bukaci Sufeto-Janar na ‘yan sandan da ya dakatar da Sufeto Simon Agrigba da Sufeto John Nuhu bisa ga ikon Tawagar.
Wasikar ta kara da cewa:
“An kuma bukaci IGP da ya sanar da Hukumar kan damke ASP John Umoru wanda a halin yanzu ake nema a duk lokacin da aka kama shi domin ta dauki matakin da ya dace.”
Hukumar ta kuma umurci Sufeto Janar na ‘yan sandan da ya yi mata karin bayani kan lamarin domin daukar matakin da ya dace.
Harkallar kwaya: Abba Kyari ya yi fallasa, NDLEA ta je kotu neman ci gaba da tsare shi
A wani labarin, jaridar Punch ta ruwaito cewa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar tare da wasu 'yan tawagarsa mutane hudu na iya ci gaba da zama a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA).
A cewar jaridar, hukumar ta garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta sanar da kotun aniyar ta na tsare wadanda ake zargin sama da awanni 48 da aka kayyade.
Da take zantawa da wata majiya mai tushe a hukumar, Punch ta bayyana cewa Kyari ya yi wasu bayanai da za su kai ga kara bincike don haka hukumar ta NDLEA ba za ta iya gurfanar da shi a gaban kuliya ba.
Asali: Legit.ng