Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

  • Wata kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani mutumin da ya kashe 'ya'yan cikinsa tagwaye
  • Wannan na zuwa ne shekaru 5 bayan da mutumin ya kashe yaran, lamarin da ya kai zuwa kotu don shari'ar
  • Rahoton da muka samo daga jaridar The Nation ya bayyana yadda mutumin ya tursasawa kansa kashe 'ya'yan nasa

Akamkpa, jihar Kuros Riba - Kotu a yankin Akamkpa da ke jihar Kuros Riba ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani Anyabime Festus Udo bisa laifin kashe ‘ya’yansa mata tagwaye guda biyu.

Festus, a 2017, ya sanya wa 'yan mata, Mfoniso Anyanime da Emediong Anyanime guba a abin sha, yana mai da'awar cewa su mayu ne kuma silar "wahalarsa".

Kara karanta wannan

Matashi a Kano,Tijjani, ya sha fiya-fiya bayan samun labarin budurwarsa zata auri maikudi

Ya kashe 'ya'yansa, zai yi mutuwar wulakanci
Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har ya mutu | Hoto: punchng.con
Asali: UGC

Mai shari’a Agness Onyebueke ta ce kisan tagwayen shaidanci ne, kuma rashin imani hakazalika kuma ya wuce tunanin dan Adam a ce uba ya kashe dansa.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa a ranar 10 ga watan Junairun 2017, mai laifin ya baiwa ‘ya’yansa ‘yan shekara 11 abin sha hade da duba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya ta mutu nan take yayin da ta biyun ta rarrafa kan hanya inda wani ya cece ta daga bisani ta mutu washegari a asibiti.

Dan rajin kare hakkin yara na kungiyar BRCI, James Ibor, Esq. ya yaba da hukuncin, yana mai cewa ya zo ne jim kadan bayan Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashe da su dauki matakan yaki da cin zarafin yara da ke da alaka da bokanci da tsafi.

Ibor ya ce ‘yan sanda sun kama Udo ne bayan bincike, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Ya kara da cewa:

“’Yan sanda sun tabbatar da cewa an gudanar da binciken lafiya da na gawarwakin yaran da suka mutu wanda hakan ya taimaka wajen yanke hukunci.
"Wannan hukunci babbar nasara ce ga wadanda abin ya shafa, Mfoniso Anyanime, Emediong Anyanime, da kuma musamman gwamnatin Kuros Riba."

Kotu ta yanke wa wani tsohon Sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya

A wani labarin, wata babbar kotu dake Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, ranar Litinin, ta yankewa Damilola Olasoji, tsohon sojan Najeriya da aka sallama daga aiki, da kuma Koiki Benson, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Premium Times ta tattaro cewa kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin ne bisa kama su da aikata laifin fashi da makami.

Yan sanda sun shaida wa kotun cewa a ranar 30 ga watan Maris, 2016, Olasoji, Benson da kuma Ogbesetuyi Tunde, suka haɗa kai suka farmaki Oluwadare Adebayo a gidan mai dake Ado-Ado, suka saci miliyan N1.2m.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.