Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nasarawa kisar gilla a hanyar Jos
- Wasu bata gari da ba a gano ko su wanene ba sun sake tare matafiya 'yan jihohin Kano da Nasarawa a hanyar Jos
- Miyagun sun halaka a kalla mutane hudu cikin matafiyan sannan suka raunata wasu da dama tare da lalata motoccinsu
- Rundunar yan sandan jihar Plateau ta bakin kakakinta ASP Uba Gabriel ta tabbatar da harin amma ta ce mutum biyu ne aka kashe
Plateau - A kalla mafiya hudu ne aka kaiwa hari tare da kashe su yayin da wasu da dama suka jikkata a safiyar ranar Laraba a Bida Bidi Junction a karamar hukumar Jos ta Arewa, Jihar Plateau.
Daily Trust ta rahoto cewa harin ya faru ne misalin karfe 12 na dare a cewar wadanda suka tsira.
Dukkan matafiyan yan asalin jihohin Kano ne da Nasarawa.
Matafiyan sun baro Kano ne suna hanyarsu ta zuwa jihar Nasarawa yayin da bata garin suka tare babban hanyar Zaria suka musu duka suka sare su da adduna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An garzaya da wadanda suka tsira zuwa Asibitin Bingham, a Jos don a kula da su.
An kona motan da ke dauke da matafiyan yayin da sauran motoccin kuma aka lalata su kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yan sanda sun tabbatar da harin
Kakakin yan sandan Jihar Plateau, ASP Uba Gabriel, ya tabbatar da afkuwar harin amma ya ce mutum biyu ne kawai suka tabbatar da rasuwarsu.
Ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar 'ya isa wurin da abin ya faru domin dawo da doka da oda.'
Harin na zuwa ne awanni biyu bayan kashe wasu masu hakar ma'adinai a garin Yelwa a ranar Talata.
An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona
A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.
Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.
Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.
Asali: Legit.ng