Kotu: Mai aski zai yi sharar caji ofis na kwana 90 saboda samunsa da laifin damfarar kudi ta intanet
- Wata babbar kotun Kubwa da ke Abuja a ranar Laraba, ta umarci wani mai aski mai shekaru 21, Isaac Clement da ya share ofishin ‘yan sanda na kwana 90
- Hakan ya biyo bayan damfarar yanar gizon da hukumar yaki da rashawa, EFCC ta gano Clement ya aikata, sai dai ya bukaci kotun ta yi masa rangwame
- Alkalin ya bukaci matashin da ya dinga zuwa yana sanya hannu kullum a lokacin da zai fara sharar da kuma lokacin da ya kammala, sannnan ya kasance mai kyawawan dabi’u
FCT, Abuja - A ranar Laraba, babbar kotun Kubwa da ke Abuja ta umarci wani mai aski, Isaac Clement mai shekaru 21 da ya dinga share ofishin ‘yan sanda na tsawon kwana 90, Vanguard ta ruwaito.
Clement wanda ya amsa laifin damfarar yanar gizo wanda hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta zarge shi da aikatawa, ya kuma bukaci kotu ta yi masa rangwame.
Alkali Kezziah Ogbonnaya, yayin yanke hukunci, ya umarci matashin da ya fara sharar caji ofis din a ranar Alhamis.
Alkalin ta bukaci Clement da ya dinga sanya hannu kullum kafin ya fara sharar da kuma bayan ya kammala.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkalin ya ja kunnen shi inda yace ya kasance mai kyawawan dabi’u
Ogbonnaya ya ja kunnen Clement inda ya bukaci ya kasance mai kyawawan dabi’u kuma ya kiyaye aikata laifuka makamantan hakan.
Kamar yadda Vanguard ta bayyana, tun farko lauyan EFCC, Rita Ogar ta sanar da kotu cewa lauyan wanda ake kara, Patrick Onuh ya bukaci rangwame wanda dukan su suka sanya hannu a wata takarda a ranar 4 ga watan Fabrairu.
Ogar ta bukaci kotun ta yanke wa Clement hukuncin da ya dace da laifin shi.
Ta sanar da kotu cewa Clement ya yi damfara a matsayin Mr Parthner Smith, sojan Amurka, inda ya yashi dala 550 daga hannun wata ‘yar kasar Amurka, Felicia Mendez.
Ya amshi kudin da sunan zai siya tikitin jirgin da zai kai mata ziyara
A cewarta, ya yaudari Mendez akan cewa da kudin zai siya tikitin jirgi don ya kai mata ziyara a watan Augustan 2021.
Laifin a cewarta ya ci karo da sashi na 320 na Penal Code kuma hukuncin sa yana karkashin sashi na 322.
Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi
A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.
An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Yan sandan suna zarginsa da:
"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".
Asali: Legit.ng