Abin mamaki: Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata
- Ministan Buhari ya bayyana cewa, yajin aikin ASUU abin mamaki ne, sannan ya ce nan ba da jimawa ba za a samu mafita
- Ministan ya bayyana haka ne lokacin da yake gana wa da manema labarai a Abuja yau Laraba 16 ga watan Fabrairu
- Ministan ya ce abin mamaki ne tafiyar ASUU yajin aiki, don haka ba laifin gwamnati bane, laifin ASUU ne kawai
FCT, Abuja - Adamu Adamu, ministan ilimi, ya ce matakin yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) na wata daya "abin mamaki ne"
Ya ce ba laifin gwamnatin tarayya ba ne idan har ba a cimma matsaya ba bayan tattaunawa da dama tsakanin bangarorin biyu, TheCable ta ruwaito.
Ministan ya yi wannan magana ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Adamu ya ce ASUU ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne ba zato ba tsammani a dai dai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
“ASUU, abin takaici, sun tafi yajin aiki kuma ina neman su saboda a magance duk matsalolin.
“Abu na karshe da ya faru shi ne kwamitinmu ya duba bukatunsu amma ana cigaba da tattaunawa. Sun gabatar da daftarin yarjejeniya wanda ma'aikatar ke dubawa.
“Wani kwamiti yana dubawa. Idan ya kammala, gwamnati a shirye take ta sanar ta amince. Sai kwatsam na ji sun tafi yajin aiki.”
Dalilin rashin halartar minista taron ASUU
Dangane da zargin da ASUU ta yi kan rashin halartar ministan taronta, ya ce:
“ASUU ba za ta taba fadin haka ba. Kullum nakan kira taron da kaina. Tarukan da ban halarta ba su ne wadanda suka yi sa’ad da nake asibiti a Jamus.
“Muna son a cimma matsaya cikin lumana. Gwamnatin tarayya a shirye ta ke ta gana da su a kan dukkan batutuwan da suka tattauna sannan idan aka yi taruka da yawa kuma gibin bai rufe ba, to ina ganin ba laifin gwamnati ba ne.
“Akwai mafita kan wannan. Tattaunawar ita ce mafita, shi ya sa na ce na yi mamaki da ASUU ta shiga yajin aiki.”
Da yake magana kan lokacin da za a cimma matsaya, ministan ya kara da cewa:
“Ba zan iya ba ku lokaci ba. A shirye nake na cimma matsaya da ASUU a yanzu amma tunda ba ni kadai bane, ba zan iya ba ku lokaci ba amma tabbas za mu cimma matsaya nan ba da jimawa ba."
A hukumance: Daga karshe ASUU ta yi bayani dalla-dalla, ta shiga yajin aiki
A wani labarin, kungiyar malaman jami'a wato ASUU ta ayyana shigarta cikakken yajin aiki bayan tattaunawa mai zurfi da hukumomin zartasrwata, inji rahoton Punch.
Ta ayyana wannan yajin aikin ne a wani taron manema labarai da shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke ya hada, inda ya yi jawabi dalla-dalla kan batun a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.
Mambobin majalisar zartaswar kungiyar ta kasa sun gudanar da taruka kan batun yajin aikin tun ranar Asabar a jami’ar Legas mai taken, ‘NEC for NEC.'
Asali: Legit.ng