Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa

Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa

  • Majiyoyi sun bayyana yadda Sifeta Janar Alkali Baba suka gana da Marwa a wata ziyarar ba-zata da Marwan ya kai hedkwatar rundunar a Abuja
  • Bayan ganawar Marwa da Alkali, an gano cewa Alkali ya tattara manyan 'yan sandan Najeriya inda ya sanar da su abinda ke wakana
  • An gano yadda hankalin Sifeta Janar na 'yan sanda ya tashi bayan ya ji batun kuma Kyari ya yi batan dabo a garin Abuja

FCT, Abuja - Sabon labari ya bayyana a kan yadda sifeta janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba da shugaban hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), Birgediya janar Buba Marwa, suka hadu a hedkwatocin tsaro dake Abuja.

Sun yanke shawarar yadda za su bullo wa lamarin kwamandan hukumar binciken sirri na 'yan sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyari, bisa hannunsa a harkallar safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 25.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Bayanin yazo ne bayan kwana daya da 'yan sanda suka dakatar da duk wasu rassa na IRT na jihohin dake fadin kasar, wanda hakan ya biyo bayan kama DCP Kyari da aka yi.

Hakan yazo ne a jiya, yayin da manyan jami'an tsaron da suka yi ritaya suka nuna rashin jin dadin su bisa ga sa hannun DCP Kyari a harkallar safarar hodar iblis, inda suka yi kira ga 'yan sanda da NDLEA da su bankado manyan 'yan sanda da wadanda suka yi ritaya gami da 'yan siyasan da suke mara wa kwamandan IRT da aka dakatar.

Baya ga haka, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi ta fara tuhumar Kyari da sauran mutum hudun da ke da sa hannu a harkallar safarar hodar iblis.

Vanguard ta tattaro yadda wasu azzaluman yan sanda da ma'aikatan NDLEA suke da alhakin safarar miyagun kwayoyi, duk da sunkai matakai manya-manya a rundunar tun shekarar da ta gaba.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An samu labarin yadda sa hannun Kyari a harkallar safarar miyagun kwayoyi ya zama daya daga cikin manyan korafe-korafen da shugabancin Buba Marwa ya amsa.

Marwa ya bayyana a Hedkwatocin 'yan sandan ba tare da ya shaida musu zuwan shi ba

An gano bayan bidiyon yadda aka kama Kyari dumu-dumu ya riske Marwa, ya ziyarci hedkwatar 'yan sandan a ranar Alhamis ba tare da ya shaida wa kowa ba. A lokacin da IGP Alkali Baba na hanyar shi ta fita daga ofishin sa, inda aka shaida mishi cewa, an ga Marwa a harabar.

Majiyoyi sun bayyana yadda IGP ya cika da mamaki, a lokacin da shugaban NDLEA ya bayyana dalilin ziyarar tashi, sannan ya nuna mishi bidiyon yadda aka ji Kyarin yana neman sasanci da ma'aikatan NDLEA a cikin motarsu.

Washe garin ranar, (Juma'a) IGP Baba Usman ya gabatar da taro da jiga-jigan rundunar, inda ya sanar dasu game da lamarin da ke wakana, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon Sanata yana girgijewa a cikin dakinsa, ya na nuna bajintarsa a fannin rawa

Kafin nan, ya bada umarnin kama sauran ma'aikatan da ke da hannu a harkallar miyagun kwayoyi. Sun hada da ACP Sunday Ubuah, ASP Bawa James, sifeta Simeon Agrigba da John Nuhu. Yayin da aka tasa keyar su zuwa hedkwatocin 'yan sanda gami da garkame su.

Sai dai an samu labarin yadda aka nemi DCP Abba Kyari aka rasa a ranar Juma'a. Kamar yadda manema labarai suka tattaro yadda aka neme shi, wanda ya kai ga zuwa gidan shi na Abuja, da masallacin da ya saba yin sallar Juma'a, amma ba a gan shi ba.

Majiyoyi na kusa dashi sun ce, yayin da labarin kama yaran shi ya riski Kyari, an shawarce shi da ya tsere daga kasar don gudun kama shi, da kalubalen da ka iya zuwa da hakan, amma sai yayi kunnen uwar shegu.

An gano yadda aka yi ta kiran wayar wasu jiga-jigan Najeriya da su sa IGP da Marwa su cire hannun su a kan lamarin, saboda kasar Amurka na tuhumar Kyari da hada kai da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: IGP ya bada umarnin rufe dukkan sassan IRT da STS na 'yan sandan Najeriya

Majiyoyi sun tsegumta yadda Kyarin yayi batan dabo a babban rundunar 'yan sandan a daren Juma'a.

An samu labarin yadda IGP ya shiga damuwa, idan maganar batan Kyari ta bayyana, saboda gudun abinda zai jawo wa rundunar 'yan sandan.

Amma daga baya an kama Kyari a ranar Asabar, kuma aka sake maida shi wurin 'yan sandan da suka fara kama shi, daga nan ne suka mika shi ga NDLEA a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng