Daukar doka a hannu: Gwamnatin Katsina ta haramta ayyukan kungiyar ‘Yan Sa Kai’
- Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana haramta ayyukan kungiyar 'yan bangan 'Sa Kai' a fadin jihar Katsina
- Wannan haramtawar na zuwa ne yayin da 'yan bangan ke daukar doka a hannunsu ba tare da mika wa ga jami'an tsaro ba
- Gwamnati ta bayyana kungiyar 'yan bangan da ta amince da ayyukansu a jihar, da kuma yadda suke aiki
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta haramta ayyukan kungiyar ‘Yan Sa Kai Volunteer Group’ ta ‘yan banga saboda “mummunan ayyukan ta’addanci” da ke kai ga kisan gilla kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba da yawaitar sace-sace.
A wata sanarwa da mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro Alhaji Ahmed Katsina ya fitar ta ce dokar ta fara aiki ne nan take, inji rahoton The Nation.
An dai yi ta cece-kuce kan yadda kungiyar ke daukar doka a hannunta a fadin jihar Katsina da sunan yaki da ‘yan bindiga da ta’addanci.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘’Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da ayyukan kungiyar Vigilante ne kawai, wanda ke karkashin kulawa, lura da sa idon ‘yan sanda, sauran hukumomin tsaro da cibiyoyin gargajiya.
‘’Daga yanzu, a mika wadanda ake tuhuma ga ‘yan sanda ko wata hukumar tsaro domin gudanar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace. Kada kowa ya dauki doka a hannunsa, a karkashin kowane irin laifi."
A cewar rahoton Daily Post, sanarwar ta ce daga yanzu:
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro za su yi maganin duk wani mutum ko gungun mutanen da aka samu suna bayyana kansu a matsayin 'Yansakai ko wani irin suna mai kama da haka a jihar.”
'Yan bindiga sun sake addabar yankunan Katsina, an sake kulle makarantu, hakimai sun yi kaura
A wani labarin, Wazirin Katsina, Farfesa San Lugga ya bayyana cewa yawan hare-haren yan bindiga ya yi sanadiyar rufe makarantu a kananan hukumomi takwas na jihar Katsina.
Farfesa Lugga ya bayyana cewa hakiman kananan hukumomin takwas sun koma Katsina, babbar birnin jihar da zama sakamakon hare-haren.
Wazirin Katsinan ya bayyana hakan ne a garin Ilorin, jihar Kwara a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, a wajen wani taro da cibiyar zaman lafiya ta IPCR ta shirya, jaridar The Nation ta rahoto.
Asali: Legit.ng